PDP ta ƙwace kujerar Kakakin Majalisar dDokokin Yobe da ta mahaifar shugaban Majisar Dattawa

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Sakamakon da hukumar zaɓe INEC ta sanar na zaɓen ‘yan majalisar dokokin jihar Yobe, ya nuna ɗan takarar jam’iyyar PDP, Hon. Musa Lawan Majakura ya lallasa na jam’iyyar APC, wanda shi ne Kakakin majalisar, Hon. Ahmed Lawan Mirwa a mazaɓar Nguru ta waje.

Sakamakon ya nuna jam’iyyar PDP ta samu ƙuri’u 6,648 yayin da APC ta samu ƙuri’u 6,466 a zaɓen, wanda hakan ya bai wa ɗan takarar PDP nasarar lashe zaɓen.

Hon. Majakura na PDP ya lallasa Hon. Ahmed Mirwa ne bayan da ya kwashe shekaru 20 yana jan zarensa a kujerar, daga 2003 zuwa wannan lokacin, inda ya kasance Kakakin majalisar jihar daga 2019 zuwa 2023.

A hannu guda, a ƙaramar hukumar Bade ta Tsakiya, ɗan takarar jam’iyyar PDP, Hon. Saddiq Yahaya Attajiri ne ya ƙwace kujerar ɗan majalisar APC, Hon. Mohammed Kabiru Maimota, a zaɓen da ya gudana ranar Asabar.

Sakamakon zaɓen da INEC ta rattaba wa hannu, ya ayyana ɗan takarar jam’iyyar PDP ya samu ƙuri’u 12,863, inda na jam’iyyar APC, ya samu ƙuri’u 11,248, al’amarin da ya bai wa ɗan takarar jam’iyyar PDP nasara a zaɓen.