PDP ta dakatar da ɗan majalisa a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Jam’iyyar PDP a mazaɓar Dikko da ke Ƙaramar Hukumar Argungu ta dakatar da tsohon ɗan majalisar wakilai, Hon. Sani Bawa Argungu.

Wannan yana ƙunshe ne a wata takardar sanarwa mai ɗauke da sa hannun ilahirin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar na mazaɓar Dikko da ke cikin garin Argungu da aka raba wa manema labarai ranar Litinin ɗin da ta gabata 27 ga watan Yuni 2022.

Takardar ta bayyana cewa sun yanke shawarar dakatar da Honorabul Sani Bawa Argungu ne daga shiga duk wani al’amari na jam’iyyar har sai baba-ta-gani bayan wani zama da shugabannin  mazaɓar ta Dikko suka gudanar, inda aka gano ya kitsa wa jam’iyyar PDP zagon ƙasa ne a lokacin zaɓen fidda gwani na ɗan majalisar dattawa da aka gudanar 24 ga watan Mayun da ya gabata tsakanin Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi da kuma Honorabul Ibrahim Bawa Kamba, inda Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi ya samu nasarar lashe zaɓen fidda gwanin.

Haka zalika takardar ta bayyana cewa Sani Bawa Argungu ya yi uwa da makarɓiya wajen kitsa zagon ƙasa yayin gudanar da zaɓen fidda gwanin da kuma bayan zaɓen.

Haka zalika takardar ta ƙara da cewa Sani Bawa Argungu ya yi gaban kansa na ɗaukar maganar jam’iyya zuwa kotu.

Takardar ta ƙara da cewa an sanar da ƙaramar hukuma da jiha da kuma duk wanda ke da haƙƙi.

Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Honorabul Sani Bawa amma dai hakan ba ta samu ba saboda bai amsa kiran waya ba kuma bayan tura masa saƙon kartakwana har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba wata amsa.

Honarabul Sani Bawa Argungu dai ya yi ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Argungu da Augie a shekarar 1999 zuwa 2003.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *