Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Ɗan takarar neman shugabancin tarayyar Nijeriya a ƙarƙashin tutar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewar, jam’iyyar su ita ce mafi tsufa, mafi girma, kuma mafi ɗauke da yawan jama’a da za ta sake karɓan jagorancin ƙasar nan a zaɓen gamagari na watan Fabrairun shekarar baɗi, 2023.
Gwarzon na Jam’iyyar PDP ya yi waɗannan kalamai ne ranar Laraba a filin wasan ƙwallo na tunawa da Marigayi Abubakar Tafawa Balewa yayin da yake karɓan mutane fiye da 25,000 waɗanda suka canja sheƙa daga wasu jam’iyyu zuwa jam’iyyar su, inda yake cewa Jam’iyyar PDP babu inda ba ta karaɗe ba a ƙasar nan.
Atiku Abubakar wanda ya lura da cewar, babu wata jam’iyya da take da diri, karvuwa da farin jini kamar Jam’iyyar PDP, sai ya jinjina wa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed bisa ɗimbin nasarari daya cimma a fannonin rayuwa dabam-dabam a cikin shekaru uku da suka gabata ƙarƙashin mulkin Jam’iyyar PDP mafi karɓuwa ga jama’a.
Atiku ya kuma lura da cewar, cincirindon jama’a da idanuwan sa suka gani a filin wasan ƙwallo dake garin Bauchi, wata kyakkyawar manuniya ce ta PDP da Gwamna Bala Mohammed suna tare da jama’a, sai ya buƙaci a haɗa ƙarfi da ƙarfe ta yadda za a tabbatar da nasarar jam’iyyar a dukkan matakan mulki a zaɓen gamagari na shekarar 2023, idan Mahalicci ya kai mu.
Ƙasungumin direban na jam’iyyar PDP sai ya jinjina wa dakaru waɗanda suka canja sheƙar, yana mai cewar, sun yi kyakkyawar dabara da suka ƙetaro daga waɗancan burtuttunai a wannan lokaci da yaƙin neman zave ya kama gadan-gadan, kuma da ikon Allah wannan jam’iyya za ta zauni Bauchi, ta kuma riƙe kujerar jagorancin Nijeriya sakamakon zaɓen gamagari mai gabatowa.
Mai riƙe da tutar yaƙin neman kujerar shugabancin ƙarƙashin Jam’iyyar PDP sai ya karɓi tubabbun a cikin farin ciki da yakana, waɗanda daga cikin su akwai kakakin majalisar dokoki na Jihar Bauchi dake kan karaga, tsohon muƙaddashin gwamna a gwamnatin APC ta baya-bayan nan, Arc. Abdu Sule Katagum, wanda ya share fagen shiga takarar gwamna a jam’iyyar APC, Farouk Mustapha, yana mai taya gwamna, jam’iyya da jama’ar Bauchi murna bisa wannan babban kamu.
Atiku sai ya bayyana ƙwarin gwiwar cewar, cincirindon jama’a da suka hallara a wannan rana ta Laraba, idan ya dawo Bauchi ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugabanci nan bada jimawa ba, lamarin zaiyi ninkin baninkiyar haka.
“Ina son yin amfani da wannan dama domin na taya al’ummar jihar Bauchi murna bisa ɗimbin nasarori da jihar ta samu ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed a fannonin rayuwa daban-daban da suka haɗa da kiwon lafiya, bayar da ilimi, hanyoyi da wasu kayan ababen more rayuwa, yana mai cewar, “lalle Gwamna Bala da Jam’iyyar PDP sunyi rawar gani”.