PDP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomi a Taraba

Daga BASHIR ISAH

Jam’iyyar PDP a Jihar Taraba ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar kwanan nan.

A ranar Lahadin da ta gabata Hukumar Zaɓe ta Jihar Taraba, TSIEC, ta bayyana cewa PDP ce ta lashe zaɓen ciyamomi a ilahirin ƙananan hukumomi 16 da jihar ke da su, kana ta samu kansiloli guda 168.

Shugaban hukumar zaɓen jihar, Dr. Philip Duwe, shi ne ya bayyana sakamakon zaɓen a Jalingo, babban birnin jihar, inda ya ce shida daga cikin jam’iyyu 19 da aka yi wa rijista ne suka shiga zaɓen.

Dr Duwe ya yaba wa ‘yan jarida bisa aiki da gaskiya wajen yaɗa harkokin zaɓen.

“Duk da ƙalubalen da ake fuskanta, kun nuna ƙwazo, kun yi wa ƙasarku aiki yadda ya kamata,” in ji shi.