Daga BASHIR ISAH
Ɗan takarar gwamna a Jam’iyyar PDP a Jihar Ribas, Siminialayi Fubara shi ne wanda INEC ta tabbatar a matsayin wanda ya ci zaɓen jihar a zaɓen da ya gudana ranar Asabar da ta gabata.
Baturen zaɓe a jihar, Farfesa Akpofure Rim-Rukeh, shi ne ya ba da sanarwar sakamakon zaɓen a ranar Litinin da daddare a Fatakwal, babban birnin jihar.
Ya ce Fubara na PDP ya lashe zaɓen ne bayan da ya samu ƙuri’u 302,614, inda ya doke takwaransa na APC, Tonye Cole, wanda ya samu ƙuri’u 95,274.
INEC ta ce ɗan takarar SDP, Sanata Magnus Abe, shi ne ya zo na uku da ƙuri’u 46,981, yayin da ɗan takarar jam’iyyar LP, Beatrice Itubo, ya rufa masa baya da ƙuri’u da 22,224.