PDP ta maye gurbin Walid Jibrin da Adolphus Wabara a matsayin shugaban Kwamitin Amintattunta

Daga BASHIR ISAH

Babbar jam’iyyar hamayya (PDP) ta naɗa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, wato Adolphus Wabara, a matsayin shugabn Kwamitin Amintattu (BoT) na jam’iyyar.

Kodayake naɗin na riƙon ƙwarya ne, hakan ya biyo bayan murabus ɗin da Sanata Walid Jibrin ya yi ne a matsayin shugaban kwamitin.

A ranar Alhamis Jibrin ya ba da sanarwar ajiye muƙaminsa a lokacin da ake tsaka da gudanar da taron kwamitin a Abuja.

Ya ce ya yanke shawarar ajiye muƙamin nasa ne don warware wasu matsalolin da jam’iyyarsu ta PDP ke fuskanta, musamman kan abin da ya shafi shugabancin jam’iyyar don tunkarar babban zaɓen 2023.

Tun bayan da Alhaji Atiku Abubakar ya samu nasarar zama ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin PDP, jam’iyyar ta soma fuskantar matsin lamba daga ɓangarori mabambanta kan buƙatar Sanata Jibrin da Shugaban PDP na Ƙasa, Iyorcha Ayu su yi murabus daga muƙamansu.

Atiku da Jibrin baki ɗayansu ‘yan yankin Arewacin Nijeriya ne.