PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen gwamna a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Babbar jam’iyyar hamayya a jihar Katsina, wato PDP, ta yi watsi da sakamakon zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.

Babban Daraktan yaƙin neman zaɓen Lado/Atiku, Mustapha Muhammad Inuwa ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da Jam’iyyar ta kira a birnin Katsina.

Inuwa ya ce sun yi Allah wadai da sakamakon da hukumar zaɓe ta fitar a jihar. Kazalika, ya ce ba su yarda da shi ba, kuma za su garzaya kotu.

“Mun ƙi karɓar wannan zaɓen, ba mu yarda da shi ba kuma ba mu amince da shi ba a matsayinmu na jam’iyyar PDP a jihar Katsina,” inji shi.

Daraktan yaƙin neman zaɓen ya yi zargin APC ta yi amfani da kuɗi da kayan abinci ta kuma tilasta wa ma’aikatan jihar akan su zaɓe ta.

A cewarsa, APC ta lalata tsarin zaɓen da ake da shi, ta kuma yi wa dimokaraɗiyya karan tsaye yayin gudanar da zaɓen.

Ya kuma ce an hana al’umar jihar zaɓen wanda suke so.

Ya ce a tarihi ba a taɓa yin zaɓe mara inganci a Katsina da ma Nijeriya baki ɗaya irin wanda ya gudana ranar Asabar da ta gabata ba.

A ranar Lahadi hukumar zaɓe a jihar ta bayyana ɗan takarar APC, Dikko Umar Raɗɗa a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 859,892 yayin da ɗan takarar PDP, Yakubu Lado Fanmarke ya zo na biyu da ƙuri’u 486,620.