PDP ta zargi Kwankwaso da haɗama

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar PDP ta zargi tsohon gwamnan Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da yin ƙarfa-ƙarfa da babakere a zaɓen shugabannin jam’iyyar a Kano.

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, Adamu Yunusa Ɗangwani, tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai, Ɗanburam Abubakar Nuhu da Yusuf Bello Ɗambatta, Kwamishinan Ma’aikatar Ƙasa, su ne suka bi sahun sauran ‘yan jam’iyyar PDP a Jihar Kano wajen zargin tsohon mai gidan su, Sanata Rabi’u Kwankwaso da yin ƙarfa-ƙarfa a jam’iyyar.

Ɗangwani da Ɗanburam da Ɗambatta jiga-jigan ‘yan ɗariƙar Kwankwasiyya ne, kafin a kakar siyasa ta bana su raba gari da jagoran nasu, Rabi’u Musa Kwankwaso.

A wata ganawa da masu ruwa da tsaki na PDP su ka yi ranar Talata, a ofishin tsohon gwamnan Jigawa, Alh. Sule Lamido, sun yi kira ga uwar jam’iya ta ƙasa da ta rushe shugabancin jam’iyyar a jihar saboda yadda ya ke son  ya yi ƙarfa-ƙarfa.

A takardar bayan taro da Ɗambatta, tare da Akilu Sani Indabawa su ka sanya wa hannu kuma a ka raba wa manema labarai, masu ruwa da tsakin sun zargi Kwankwaso da yi wa PDP zagon ƙasa, domin ciyar da jam’iyyar NNPP da ya ke shirin komawa nan gaba.

“Yunqurin Rabi’u Kwankwaso na ƙarfa-ƙarfa a Jam’iyyar PDP yayin da a lokaci guda yake gina  kishiyar Jam’iyyar PDP wato Jam’iyyar NNPP.

“Wani salon zagon ƙasa ne Kwankwaso ke yi wa PDP a Kano, inda idan ba a tashi tsaye ba, to za a kai ƙarnin da an hana PDP fitar da ‘yan takara a zaɓen 2023 a Kano.

“Akwai lokacin tunda za a rufe siyar da fom ɗin takarar ga ‘yan takara a ranar 1 ga watan Afrilu a 2022. Taron ya tabbatar da tsoron shi, domin idan ba a ɗauki mataki ba PDP za ta rasa damar ta na tsayar da ɗan takara ta bar wa NNPP dama.”

Taron ya tattauna akan haɗin kai da zama tsintsiya maɗauri ɗaya don tabbatar da kowa an tafi da shi a tafiyar a yayin sabon shugabancin.

Saboda haka mambobin jam’iyyar a tsakanin su wanda suka haɗa da Sule Lamido tsohon gwamnan Jigawa, Aminu Wali, Tsohon Minista, Sanata Hayatu Gwarzo, Dakta Akilu Sani Indabawa, Dakta Yunusa Adamu Ɗangwani da dai sauransu.

“Mu na kira ga kwamitin zartarwa na ƙoli da ya yi gaggawar rushe shugabancin Kano, kuma su naɗa sabon kwamitin riƙo da za su gudanar da al’amuran jam’iyyar.”

Idan za a tuna, Manhaja ta rawaito cewa Kwankwaso ya ce zai sanar da sauya sheƙar sa zuwa NNPP ne a ƙarshen watan Maris ɗin nan da mu ke ciki.