Peter Mbah ya lashe zaɓen Gwamnan Enugu

Daga WAKILINMU

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ayyana ɗan takarar gwamnan na Jam’iyyar PDP a Enugu, Peter Mbah, a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ya gudana a jihar ranar Asabar da ta gabata.

INEC ta ce Mbah ya cinye zaɓen ne bayan da ya samu ƙuri’u 160,895.

Xan takarar Jam’iyyar Labour, Chijioke Edeoga, shi ne ya zo na biyu da quri’u 157,552, yayin da Uche Nnaji na Jam’iyyar APC ya zo na uku da ƙuri’u 14,575.

Baturen zaɓen, Farfesa Maduebibisi Ofo-Iwe, shi ne wanda ya bayyana sakamakon zaɓen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *