Peters ya maye gurbin Farfesa Adamu a NOUN

Daga FATUHU MUSTAPHA

Farfesa Olufemi A. Peters ya kama aiki a matsayin sabon Mataimakin Shugaban Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN) inda ya maye gurbin Farfesa Abdalla Uba Adamu wanda wa’adin aikinsa ya kammala a ranar Laraba, 10 ga Fabrairun 2021.

Da yake jawabi yayin bikin karɓar ragamar aiki da ya gudana a ranar Alhamis a Abuja, Petaers ya bayyana cewa jami’ar ba za ta taɓa mancewa da gudunmawar da Adamu ya bayar wajen cigabanta ba a zamaninsa.

Ya ce, “Zamanin Farfesa Adamu a jami’ar abu ne da ba za a manta da shi ba, kuma zai zama abin kwatance a gare mu yanzu da kuma nan gaba.

“Adamu ya yi wa’adi mai armashi sannan ya kammala cikin nasara. Ina godiya ga Allah a madadinsa bisa ƙare wa’adinsa lami lafiya da kuma irin ayyukan cigaba da ya yi wa jami’ar.

A ranar 3 ga Disamban 2020 ne aka zaɓi Petaers a matsayin wanda zai gaji Farfesa Adamu.

Tun farko sa’ilin da yake gabatar da jawabinsa na bankwana, Adamu ya nuna godiyarsa ga Allah Maɗaukaki wanda ya ƙaddare shi da jagorancin jami’ar Ya kuma ba shi ikon kammalawa cikin nasara.

Ya bayyana shekaru biyar da ya shafe riƙe da jami’ar a matsayin al’amari mai cike da faɗi-tashi wanda ya ba shi damar bada tasa gudunmawa wajen faɗaɗa sha’anin neman ilimi a Nijeriya.

Sanarwar da ta fito ta hannun Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Jami’ar, Ibrahim Sheme, ta nuna Adamu ya yi yabo tare da gode wa dukkan ma’aikatansa da suka yi aiki tare a jami’ar.

Ma’aikatan jami’ar manyan da ƙanana ne haɗa da abokan arziki suka shaida bikin.