Daga NASIR S. GWANGWAZO
Ɗan wasan baya na Ƙungiyar Barcelona, Gerard Pique, ya bayyana shirinsa na yin ritaya daga wasan ƙwallon ƙafa bakiɗaya a gobe Asabar bayan kammala wasan ƙungiyar tasa da Almeria, wanda zai zamo shine wasansa na ƙarshe a tarihi.
Pique, mai shekaru 35, ya bayyana hakan ne a kafafensa na sadarwar zamani cikin wani bidiyo a jiya Alhamis.
Ɗan wasan tsakiyar bayan dai sau uku kacal Barcelona ta saka shi a jerin ’yan wasa 11 na farko a kakar wasa ta bana, inda matasan ’yan wasa irinsu Ronald Araujo, Jules Kounde, Andreas Christensen da Eric Garcia suke gaba da shi a jerin ’yan wasan da suka fi samun wasa shi, inda yake zaman benci.
A baya dai ɗan wasan, wanda ya lashe abubuwa da dama a ƙungiyar, ya ce, da ya zauna a benci tsawon shekarar kaka, gara ya yi ritaya da doka tamaula bakiɗaya.
Daga dukkan alamu zai cika alƙawarinsa kenan gobe.