
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban Hukumar Kula da Ƴan sanda (PSC), DIG Hashimu Argungu mai ritaya, ya jaddada cewa hukumar ba za ta sake bari a yi ƙarin matsayi na musamman ba ga jami’an rundunar inda ya ce sai an gudanar da jarrabawa da kuma tanadar ababen da ake buƙata daga jami’i, kafin a yi masa ƙarin girma.
Babban jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Ikechukwu Ani ya faɗi hakan, acikin wata takarda da ya fitar a Abuja inda ya ce shugaban hukumar ya bayyana haka ne a yayin karɓar baƙoncin shugabannin ƙungiyar tsoffin ƴan sandan Nijeriya.
DIG Argungu ya ce, ba za su sake tabbatar da ƙarin muƙaman da aka yi su ba bisa tsarin doka ba.
Cin jarrabawa shi ne ginshiƙin ƙarin matsayi ga kowane ɗan sanda a hukumar, ya na mai cewa babu wani abu da sunan ƙarin matsayi na musamman a ko’ina a duniya don haka ba zai amince da shi ba.
Ya ƙara da cewa, dokar ƙarin girma ta amince da yin haka ga jami’an da suka nuna bajinta yayin gudanar da ayyukansu inda ya ce za su sanya ido a ɓangaren don tabbatar da an yi shi cikin tsarin da ya dace.
Ya kuma tabbatar da cewa, ya na alfahari da rundunar ƴan sandan Nijeriya kasancewar sa ɗaya daga cikin waɗanda suka yi wa ƙasa hidima a ƙarƙashinta, saboda haka ya ce ba zai ci amanarta ba.