Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Rahotanni daga birnin Paris na cewa akwai yiwuwar PSG za ta biya ɗan wasanta Kylian Mbappe kuɗaɗen da yawansu ya kai yuro miliyan 60 a matsayin tukwicin yabawa da biyayya ko amintakar da ke tsakaninsu.
Bayanan sun ce ƙungiyar ta París Saint Germaine za ta biya tauraron na ta maƙudan kuɗaɗen ne, muddin bai raba gari da ita har zuwa ranar 1 ga watan Agusta, duk da cewar dangantakar da ke tsakaninsu ta yi rauni matuƙa, biyo bayan ƙin tsawaita yarjejeniyarsa da ya yi da ke shirin karewa a 2024.
Yanzu haka dai ƙungiyoyi da dama ne ke neman ƙulla yarjejeniya da dan wasan na Faransa.
Tuni kuma ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiya ta gabatar da tayin yuro miliyan 300 wanda PSG ta karba.
Sai dai Mbappe ya dage kan cigaba da zama a ƙungiyar ta sa, har zuwa lokacin da yarjejeniyarsa za ta ƙare.