Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Umar Dikko Raɗɗa ya bayyana cewar ya bada umarnin raba shinkafa buhu 40,000 nan take, ga al’ummar jihar da nufin rage raɗaɗin matsin rayuwa bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
Bayanin rabon tallafin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
Gwamna Raɗɗa ya ce gwamnatinsa ta sayo shinkafar ne daga kuɗin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da jihar ta karɓa daga gwamnatin tarayya.
Ya kuma ce ya amince da kafa kwamitoci don raba shinkafar a matakan ƙananan hukumomi da mazaɓu na jihar.
Sai dai, saɓanin Naira biliyan biyar da majalisar kula da tattalin arziƙin ƙasa ta ambata tun farko bayan wani taro da ta gudanar kwanan baya.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta sayo shinkafar ne da Naira biliyan biyu da gwamnatin tarayya ta saki.
Haka zalika ya bayyana kafa kwamitocin bibiya da sa ido don ganin yadda aikin rabon shinkafar zai kasance.
Daga nan sai gwamnan Umar ya ja kunnen waɗannan aka ɗorawa alhakin rabon kayan tallafin cewa, duk wanda aka samu da ƙoƙarin cin amana a aikin rabon shinkafar, kai tsaye ko a kaikaice, to zai fuskanci fushin hukuma.