Raɗɗa ya buƙaci ‘yan Nijeriya su kawar da bambancin dake tsakanin su

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya taya al’umar Jihar Katsina da ma ƙasar nan baki ɗaya murnar zagayowar Babbar Sallah ta shekarar 2023.

A saƙonsa na Sallah, Gwamnan ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi amfani da bikin Babbar Sallah na wannan shekarar wajen farfaɗo da danƙon zumunci da ƙaunar juna a tsakanin su, ba tare da la’akari da bambancin addini, ƙabilanci ko wata aƙida dake a tsakanin su.

Ya ce, “Ba tare da la’akari da bambancin addini ƙabilanci ko wata aƙida ba, dole mu rungumi juna a matsayin abu ɗaya, ya zama wajibi mu zauna da juna lafiya da kuma samun jituwa a tsakanin mu.

“Haka ne kawai zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya, soyayaya da kuma ƙaunar juna a tsakanin ‘yan Nijeriya,” inji shi.

Ta bakin Babban Sakataren Yaɗa Labaransa, Ibrahim Kaula, Gwamna Raɗɗa ya buƙaci musulmin jihar da kuma sauran al’umar ƙasar a kan su ci gaba da yi wa ƙasar addu’o’i don samun haɗin kai, zaman lafiya da kuma curewa wuri ɗaya a wannan lokaci.

Ya kuma buƙaci al’ummar musulmi akan su saka shugaban ƙasa da gwamnoni da kuma sauran shugabanni, cikin addu’a a wannan muhimmin lokaci da shugabannin ke ta ƙoƙarin ganin sun fitar da ƙasar daga ƙalubalen da take fuskanta.

Kazalika, ya kuma buƙaci al’ummar musulmi da su kalli lokacin Babbar Sallah fiye da wani lokaci na shagulgula da yanka dabbobin layya domin raba wa danginsu kaɗai, sai dai ya yi kira gare su da su faɗaɗa ranar wajen ƙoƙarin kyautatawa gami da tallafa wa gajiyayyu da marasa ƙarfi tare da waɗanda matsalar tsaro ta rabo da muhallansu.

Ya kuma ce” Ku yi koyi da Annabi Ibrahim wanda ya nuna tsantsar biyyayyar sa ga Mahaliccin mu Allah SWT tare da bin umarninSa na amincewa ya yanka ɗans, Annabi Isma’il.

Daga ƙarshe, Raɗɗa ya roƙi al’uma da su ci gaba da jajircewa wajen kiyaye dokoki da kuma ƙa’idojin addinin Musulunci domin samun rabauta a nan duniya da kuma lahira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *