Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya miƙa wa Majalisar Dokokin jihar jerin sunayen mutane 20 domin tantance su a matsayin waɗanda za su shugabanci ma’aikatu daban-daban a jihar.
Sunayen wanda mai taimaka wa gwamnan kan kafofin yaɗa labarai ya aike wa Majalisar a ranar Laraba sun haɗa da tsoffin kwamishinoni biyar na gwamnatin da ta gabata.
A yayin zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin Kakakinta, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, an bayyana sunayen kwamishinoni 20 da kuma wasu shugabannin hukumomi biyu da suka haɗa da hukumar tattara kuɗin haraji ta jiha wadda aka bayar da sunan Farfesa Sani Abubakar Mashi da kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jiha da aka bayar da sunan Garba Ɗahiru Bindawa.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon. Shamsuddeen Abubakar Dabai ne ya bayyana sunayen kwamishinonin dake ƙunshe a takardar a zauren majalisar.
Sunayen waɗanda aka miƙa wa majalisar domin tantancewa su ne:
(1) Prof. Ahmed Muhammad Bakori, daga Ƙaramar Hukumar Bakori.
(2) Ishaq Shehu Dabai daga Ƙaramar Hukumar Ɗanja.
(3) Prof. Badamasi Lawal Charanci daga Ƙaramar Hukumar Charanci.
(4) Dr. Nasiru Mu’azu Ɗanmusa daga Ƙaramar Hukumar Ɗanmusa.
(5) Malam Bala M. Salisu daga Ƙaramar Hukumar Zango .
(6) Prof. Abdul Hamid Ahmed daga Ƙaramar Hukumar Mani.
(7) Hon. Musa Adamu Funtua daga Ƙaramar Hukumar Funtua.
(8) Alhaji Yusuf Rabi’u Jirdede daga Ƙaramar Hukumar Mai’adua.
(9) Hon. Aliyu Lawal Zakari daga Ƙaramar Hukumar Dutsi.
(10) Hon. Bishir Tanimu Gambo daga Ƙaramar Hukumar Dutsinma.
(11) Hon. Hamza Suleiman Faskari daga Ƙaramar Hukumar Faskari.
(12) Alhaji isa Muhammad Musa daga Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara.
(13) Engr. Dr. Sani Magaji Ingawa daga Ƙaramar Hukumar Ingawa.
(14) Dr. Faisal Umar Kaita daga Ƙaramar Hukumar Kaita.
(15) Alhaji Bello Husaini Kagara daga Ƙaramar Hukumar Ƙafur.
(15) Hajiya Hadiza Ƴar’adua Tuggar daga Karamar Hukumar Katsina.
(17) Hajiya Zainab M. Musawa daga Ƙaramar Hukumar Musawa.
(18) Alhaji Musa Na Habu daga Ƙaramar Hukumar Daura.
(19) Dr. Bishir Gambo Saulawa daga Ƙaramar Hukumar Katsina.
(20) Barr. Fadila Muhammad Dikko daga Ƙaramar Hukumar Kurfi.
Babban mai taimakawa gwamnan kan kafofin yaɗa labarai ya bayyana waɗanda aka aike da sunayen nasu a matsayin ƙwararru masu tarin basira a fannoni daban-daban, waɗanda a cewar sa zasu kawo wa jihar cigaba.
Saboda haka ne ya bayyana su a matsayin waɗanda zasu bayar da abun da ake buƙata a ma’aikatun da za’a tura su bayan majalisar ta kammala aikin tantance su.
“Za su yi aiki kafaɗa da kafaɗa tare da gwamna da sauran masu ruwa da tsaki a jihar, domin cika alƙawuran gwamnati,samar da kyakyawan shugabanci gami da inganta rayuwar al’umar jihar Katsina,” inji shi.