Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya rantsar da kwamishinoni da masu ba shi shawara ta musamman su 38 da za su kasance ‘yan majalisar zartarwar jihar.
A bikin rantsuwar da ya gudana a filin taro na ‘Peoples’ Square, Katsina, an rantsar da kwamishinoni 20 da masu ba Gwamna shawara ta musamman su 18.
A jawabin gwamna Raɗɗa ya hori waɗanda aka rantsar ɗin da su sani cewa amana ce aka damƙa musu, don haka suke da buƙatar su tsare ta kamar yadda Allah Ya buƙata.
Gwamnan ya tabbatar musu da cewa ba zai bar kwamishina ya dawwama a ma’aikata ɗaya ba, zai riƙa sassauya su lokaci bayan lokaci daga wannan ma’aikata zuwa waccan don jihar Katsina ta amfana da ɗumbin ilmi da basirar da Allah Ya huwace musu.
Daga nan sai ya buƙace su da cewa, duk wanda aka naɗa muƙamin, al’ummarsa ne suka naɗo shi, domin suna da amannar cewa zai ba su gudunmuwa yadda ya kamata, don haka, akwai buƙatar su yi ɗamarar sauke nauyin al’ummarsu yadda ya dace.
Gwamnan ya kuma hankalinsu dangane da ƙailula wajen zuwa aiki ko zuwa makare. Inda ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta riƙa bibiyar dukkanin ayyukan da aka ba su.
Ya kuma bayyana cewar gwamnatinsa na shiri na musamman domin fito da hanyoyin samar da tallafin da zai rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da ake ciki.
Ta fuskar tsaro kuwa, Raɗɗa ya ce gwamnatinsa ta gaza zaune ta gaza tsaye, wajen ganin ta samo hanyoyin da mutanen Jihar Katsina za su zauna lafiya a yankunansu, musamman a karkara.