Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya saka hannu a kan yarjejeniyar fahimtar juna da Hukumar Raya Ƙasa ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNDP don ƙaddamar da cibiyar bayar da kariya a Arewa maso Yammacin Nijeriya.
Taron mai ɗumbin tarihi ya gudana ne a ɗakin taro na Majalisar Ɗinkin Duniya dake Abuja.
Cibiyar samar da tsaro yankin Arewa maso yamma shiri ne na hukumar UNDP Nijeriya.
Ma’aikatar harkokin waje da ofishin jakadancin Norway ne ke ɗaukar nauyin shirin dake da nufin tallafa wa jihohin Sakkwato, Zamfara, da Katsina.
Shirin na neman yin amfani da matakan ba da kariya don ƙarfafa matakan tsaro a yankin Arewa maso Yamma, da kuma yin amfani da tsarin sauyin yanayi da tsarin rayuwa mai ɗorewa don kare tashe-tashen hankula a jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da rikici.
Idan aka yi la’akari da waɗannan, hukumar UNDP ta yi alƙawarin tallafa wa don aiwatar da shirin da kuɗi Dala milyan 13,000,000 a faɗin jihohin Arewa maso Yamma guda uku da suka haɗa da Sakkwato, Zamfara, da Katsina.
Gwamna Raɗɗa da yake bayyana jin daɗinsa da wannan yarjejeniyar, ya ce shirin wani mabuɗi ne mai inganci da zai bude hanyar magance matsalolin tsaro da ke addabar jihar Katsina a halin yanzu.
A cewarsa, gwamnatinsa na buƙatar tallafi domin sake gina ‘yan gudun hijra da kuma mayar da su matsugunansu na asali da kuma tabbatar da cewa sun samu zaman lafiya.
Don cimma wannan, za a ɓullo da salo da dabarun daban-daban don yaƙar ta’addanci a jihar.
Ya kuma bayyana gamsuwar sa ga hukumar UNDP da sauran ƙasashen da ake haɗa hannu da su na goyon bayan wannan muhimmin shiri.
Ya kuma yaba wa shirin tare da tabbatar wa dukkan sauran waɗanda suke ba da gudunmuwa ga shirin cewa gwamnatinsa a shirye take na ganin aikin ya samu gagarumar nasara.
Mr. Ashraf Usman, shugaban ofishin shiyyar Arewa maso Yamma, ya bayyana cewa hukumar UNDP ta samu ƙwarin guiwa ne sakamakon sabunta himmar haɗin gwiwa da gwamnonin jihohi suka nuna a yunƙurinsu na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihohinsu.
Don haka ya taya jihohin Sokoto, Zamfara da Katsina murnar ƙaddamar da wannan muhimmin aiki a hukumance tare da fatar aiwatar da shi ya yi matuƙar tasiri a faɗin jihohin.
Waɗanda suka halarci taron su ne jakadan Jamus, H. E. Amb Annett Gunther; Jakadan Norway, H. E. Amb Knut Elliv Lein; wakilan mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro da gwamnonin Zamfara da Sakkwato da sauran manyan jami’an gwamnati daga jihar Katsina.