Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya taya Shugaban Ƙasar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu murna dangane da nasarar da ya samu a kotun sauraren ƙararrakin zaɓe, inda kotun ta tabbatar da nasarar zaɓen da aka yi wa Shugaba Tinubu tare da korar ƙarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour Party suka shigar, inda suke ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar farkon shekarar nan.
Raɗɗa ya bayyana cewar hukuncin kotun ya ƙara tabbatar da zaɓen da ‘yan ƙasar nan suka yi wa Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar ranar 25 ga watan fabarairu,2023.
“Hukuncin kotun ya tabbatar da zaɓen da ɗaukacin ‘yan Nijeriya suka yi maka, a matsayin shugaba na gari wanda ƙasarmu ta cancaci samu a wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arziki.
“Duba da tabbatar da nasarar ka da kotun sauraren ƙararrakin zaɓe ta yi, na tabbatar an kawar da dukkan wani shakku na sahihancin zaɓen nan take.
“Haka zalika aikin gina babbar ƙasa mai cike da samun ƙaruwwar arziƙi ga al’umar Najeriya a qarqashin jagorancinka yana nan kamar yadda
ake fata,” Inji Gwamnan.
Raɗɗa ya kuma bayyana cewar ‘yan Najeriya da ma al’umar duniya suna cike da matuƙar farin ciki duba da yadda shugaban ƙasar ya tafiyar da ƙasar a cikin kwanaki 100 na mulkinsa.
“A madadin mutane da gwamnatin jihar Katsina muna ƙara taya ka murnar samun nasara a kotun sauraren ƙararrakin zaɓe, kuma muna qara kiranka da kada ka kauda kai daga ƙudurinka na canja munanan kalamai da ake yi wa Nijeriya, kamar yadda ka fara aiwatarwa ta hanyar samar da manufofi da shirye-shiryen da za su taimaki al’uma wanda gwamnatinka ta ƙaddamar a kwana 100 da kama mulki.”
Daga qarshe gwamna Raɗɗa ya yi wa Shugaba Tinubu addu’ar Allah Ya ƙara yi masa jagora tare da lulluɓe shi da rahmarSa, jinƙai da kuma hikima domin ci gaba da jagorancin ƙasar nan.