Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya ce zai kafa sashen bincike da sa ido kan gudanar da harkokin kashe kuɗaɗen ƙananan hukumomi a jihar.
Sanarwar ta fito daga babban daraktan yaɗa labarai na gwamnan Muhammad Kaula ya ce gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yake karɓan rahoto a kan yadda zaɓen ƙananan hukumomi ya gudana.
Ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na gudanar da mulki bisa gaskiya da riƙon amana.
“Muna shirin gyara dokokin da ake da su yanzu da kuma kafa sashin bincike da zai sa ido kan yadda ake amfani da kuɗaɗen gwamnati yadda ya kamata”inji gwamnan.
Gwamnan ya bayyana cewa za a naɗa wani mai ba da shawarar na musamman don kula da sashin bincike,wanda aka tanadar da kayan aiki masu mahimmanci don gudanar da ayyuka yadda ya kamata.
“Wannan shiri yana bisa tubalin da aka shimfiɗa a lokacin mulkin marigayi Umaru Musa Yar’adua”inji Dikko Raɗɗa.
Gwamnan ya ce lokacin da yayi aiki a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Charanchi,”Mun ga tasiri da ingantattun ƙananan hukumomi ke da shi, kuma zamu yi don dawo da wannan matakin inganci da gaskiya”gwamnan bayyana haka.
Ya kuma yi tsokaci kan zaɓen ƙananan hukumomi da ya gudana inda yace a yanzu Katsina tana ɗaya daga cikin jihohi na farko a Nijeriya da suka yi nasarar aiwatar da miƙa mulki daga zaɓaɓɓiyar gwamnatin ƙaramar hukuma zuwa wata.
Ya nuna jin daɗin sa da halartar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da tsafin gwamnoni, manyan jami’an gwamnati da ɗaukacin al’ummar jihar, waɗanda suka fito domin kaɗa ƙuri’u.
Tun da farko da yake miƙa rahoton sa, shugaban kwamitin zaɓe da gwamnati ta kafa, mataimakin Gwamna Farouk Lawal Joɓe dukkan yan takarar APC suka lashe zaɓen da gagarumin rinjaye.