Daga BELLO WANG
Yanzu haka ana gudanar da “Taruka 2”,wato tarukan shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar ƙasar Sin da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar ƙasar, a birnin Beijing. Inda mahalarta tarukan suke tattara ra’ayoyin jama’a da buƙatunsu, tare da miƙa su ga manyan jami’an ƙasar. Wannan wani muhimmin ɓangare ne na tsarin Dimokuraɗiyya na ƙasar Sin.
Da muka tabo maganar Dimokuraɗiyya, mun san ƙasashe daban daban sun fi kwaikwayon tsarin Dimokuraɗiyya na ƙasashen yamma. Sai dai mene ne asalin tsarin Dimokuraɗiyya na Sin? Game da wannan tambaya, za mu iya neman amsarta daga cikin wasu tsoffin littattafan ƙasar Sin.
Cikin wani tsohon littafi mai suna “Li Ji”, an rubuta cewa “Duk wata ƙasa ta daukacin jama’arta ce”, inda aka bukaci mai mulki da ya zabi masu hazaƙa da ƙwarewa daga cikin al’umma, domin su taka rawa a harkokin mulki.
A cikin wani littafi mai suna “Shang Shu”, an bayyana cewa “Jama’a tushe ne na wata ƙasa”. Sa’an nan wani shehun malami na ƙasar Sin mai suna Mencius ya karɓi wannan tunani, inda ya bayyana shi sarai kamar haka: “Jama’a sun fi daraja. Filayen ƙasa tana biyo baya. Yayin da sarki ba shi da muhimmanci.”
Tunanin Dimokuraɗiyya ya ƙunshi ra’ayin samun zaman daidaito tsakanin mutane. An fara samun ra’ayi na zaman daidaito daga cikin tunanin shehun malami mai suna Confucius, wanda ya bayyana cewa “Duk wani abun da ba a son shi, kar a aikata shi kan sauran mutane”. Shi ma Mencius ya ce, “Ya kamata a girmama dattawa na kansa da na sauran mutane, da kula da yaransa da na sauran mutane”.
Ban da wannan kuma, a cikin wani tsohon littafi mai suna “Guo Yu”, an bayyana ra’ayi na kare ‘yancin mutum na fadin albarkacin bakinsu. Inda aka ce, “Hana jama’a yin magana, tamkar toshe hanyar kogi ne. Idan an toshe hanyar kogi, za a ji raɗaɗin ambaliyar ruwa. Idan an hana mutane magana, za a faɗa cikin mawuyacin hali, bayan da fushinsu ya haifar da rikici.”
Sa’an nan wani littafin da ya fi tsufa a ƙasar Sin mai taken “Yi Jing”, ya ayyana darajar tsarin Dimokuraɗiyya kamar haka: “Idan mai mulki yana yin musayar ra’ayi da jama’a, za su cimma matsaya kan manufofin ƙasa. Amma idan mai mulki ya ki sauraron ra’ayin jama’a, to, mulkin ya zo ƙarshensa.”
Waɗannan tunani game da kare haƙƙin jama’a, da tabbatar da ‘yancinsu a fannin mulki, sun riga sun zama wani muhimmin ɓangare na al’adun ƙasar Sin, wanda ya kasance asali na tsarin Dimokuraɗiyya na Sin, daidai da yadda tunanin Dimokuraɗiyya na ƙasashen yamma ke samun asali a garuruwan tsohuwar Girika.
Tabbas, tunani da tsare-tsaren yammacin duniya, su ma sun yi tasiri kan tsarin Dimokuraɗiyya na ƙasar Sin. Cikin shekaru fiye da ɗari ɗaya da suka gabata, al’adun ƙasashen yamma sun kutsa kai cikin ƙasar Sin, bisa taimakon ƙarfin sojan su, abun da ya tilasta wa Sinawa yin gyare-gyare kan harkokin siyasar ƙasar. Inda suka kifar da sarki, da shigar da tsarin “Capitalism” na jari hujja, kafin daga bisani su ƙaddamar da juyin-juya hali na Gurguzu, da tabbatar da tsarin Dimokuraɗiyya irin na Gurguzu. Har zuwa yanzu, wata babbar manufar da masu mulki na ƙasar Sin suke dauka ita ce “Yin gyare-gyare a cikin gida”.
Ta hanyar yin nazari kan tarihi, za mu iya sanin cewa, Sinawa sun gaji al’adunsu na gargajiya masu kunshe da ra’ayi na Dimokuraɗiyya, kana sun koyi abubuwa masu kyau na tsarin Dimokuraɗiyya na zamani na ƙasashen yamma. Ban da wannan kuma, suna ta aiwatar da gyare-gyare kan tsarinsu, don ya zama mai dacewa da zamani, ta yadda suka samu wani tsarin Dimokuraɗiyya mai salon musamman na kansu. Wannan tsarin Dimokuraɗiyya yana da amfani sosai, saboda ya dace da yanayin da ƙasar ke ciki, wanda yake taka muhimmiyar rawa a fannonin ciyar da tattalin arzikin ƙasar gaba, da samarwa al’ummar ƙasar alfanu. Ganin haka ya sa Sinawa ke da imani kan tsarin Dimokuraɗiyyar su.