Rahoto ya nuna yadda ake samun ƙaruwar nuna wariya ga ’yan Asiya a Amurka

Daga CMG HAUSA

Ƙungiyar nazarin haƙƙin bil adama ta ƙasar Sin ta fidda rahoto a yau Juma’a, wanda ke nuna cewa, ana samun ƙaruwar nuna wariya ga al’ummu ’yan asalin Asiya a ƙasar Amurka.

A cewar rahoton, har yanzu Amurka tana tinkaho da matsayinta na ƙasa mai hallayar nuna fifiko a tsakanin Amurkawa farar fata mafiya rinjaye, da sauran kananan ƙalibun ƙasar.

Rahoton ya ce, Amurkawa ’yan asalin Asiya, da Amurkawa ’yan asalin Afrika, da ’yan Latino da kuma Amurkawa ’yan asalin Indiya, suna fuskantar nuna wariya da ƙyama a fannoni daban-daban, kuma ba sa iya samun cikakken haƙƙoƙinsu yadda ya kamata.

Rahoton ya ƙunshi ɓangarori kamar haka, Amurkawa ’yan asalin Asiya suna fuskantar hare-haren nuna wariya yayin da aka samu ɓarkewar annobar COVID-19, kuma nuna wariya ga Amurkawa ’yan asalin Asiya ba wai ya takaita saboda annobar ba ne, akwai wasu dalilai da dama da suka ƙara ta’azzara nuna wariyar ga ’yan Asiya ta hanyar fakewa da annobar COVID-19.

A cewar rahoton, ana iya cewa, bayan kawo ƙarshen annobar, ko da batun nuna wariya ga ’yan Asiya ya ragu, mai yiwuwa ne hare-haren da ake ƙaddamarwa kan Amurkawa ’yan asalin ƙasar Sin zai iya ci gaba da karuwa, sakamakon tasirin ’yan siyasar Amurka dake nuna kiyayya ga ƙasar Sin, inda aka bukaci ɗaukar matakai mafi dacewa bisa tsarin ƙasa da ƙasa domin daidaita batun.

Mai Fassarawa: Ahmad Fagam