Daga BELLO A. BABAJI
Babban Asibitin Fadar shugaban ƙasa ya ce rahoton ɓangaren lafiya na fama da matsalolin rashin cika aiki sakamakon ƙarancin horarrun jami’an lafiya.
A cewar sa, jami’ai kaɗan ne ke aiki a rassa da dama na asibitin wanda hakan ya haifar da jira na tsawon lokaci ga marasa lafiya kafin a kawo musu ɗauki da kuma ƙaruwar sauye-sauyen rahotanninsu.
Cikin rahoton da ya fitar, asibitin ya ce sauya rahotonnin marasa lafiyar na faruwa ne sakamakon rashin samun horon da ake buƙata daga jami’an da hukumar gudanarwa ta asibitin ta turo.
An samar da asibitin ne a shekarar 1976 don ya bada kulawar lafiya ga shugaban ƙasa da mataimakinsa da iyalansu da ma’aikatan da ke aiki a fadar wanda a farko an gina shi ne a Barikin Dodon da ke Legas wanda daga bisani a 1992 aka mayar da shi Abuja.
Wani ma’aikaci da ke da kusanci da ayyukan asibitin, ya ce tuni Fadar shugaban ƙasar ta fara ɗakko hayar likitoci da wasu horarrun jami’ai don cike giɓin da ake samu.
Akan haka ne, Sakataren Fadar, Olufunsu Adebiyi ya ce akwai shirin ɗaukar matakan gyara game da asibitin wanda ake fatan ya kammala nan da watan Nuwamba, 2024.
A lokacin da kwamitin ayyuka na musamman na Majalisar Wakilai ya ziyarci Fadar, Adebiyi ya ce ayyukan zamanantar da asibitin za su taimaka wajen inganta harkokin gudanarwarsa.