Ramadan 2021: Sau ɗaya aka amince maniyyata su yi Umura

Daga WAKILINMU

Ma’aikatar Kula da Harkokin Hajji da Umura ta Ƙasar Saudiyya ta bada sanarwar cewa sau ɗaya tak za a bai wa maniyyata damar gabatar da aikin Umura a wannan lokaci.

A cewar jaridar Saudi Gazette, masu ibada na iya samun zarafin gabatar da salloli kulliyaumi a masallacin Ka’aba.

Ma’aikatar ta ce maniyyatan da suka rigaya suka samu izinin yin Umura kada su sake shiga tsarin neman wani izinin har sai wa’adin izinin farko da suka samu ya ƙare.

Yayin da kuma izinin gabatar da sallah a Masallacin Ka’aba zai yi amfani ne na yini guda wajen bai wa maniyyaci damar gabatar da kamsu salawat. Sai dai ana da daman neman izinin fiye da sau guda a cikin wannan wata mai alfarma da ake ciki, in ji ma’aikatar.

Haka nan, ma’aikatar ta ce izinin gabatar da sallar Issha zai bai wa masu ibada damar sallatar sallar Tarawihi.

A Litinin da ta gabata hadimin masallacin Ka’aba da na Madina, Sarki Salman, ya bada odar taƙaita sallar Tarawihi daga raka’a 20 zuwa raka’a 10 a Masallacin Makka da Madina a wannan Ramadan ɗin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *