
Daga BELLO A. BABAJI
Kwamitin jami’an tsaron haɗaka na zaman lafiya da gyaran tarbiyyar matasa a Jihar Kano, a wani atisaye da ya gudanar, ya yi nasarar kama ƴan daba 28 da ƙwato wasu muggan makamai gami da haramtattun ƙwayoyi.
Jami’an sun gudanar da atisayen ne a tsakanin ranakun 3 da 13 ga watan Maris, waɗanda daga cikin su akwai na hukumomin ƴan sanda, NDLEA, DSS, NSDCDC (Civil Defense), gyaran hali, shige-da-fice da kuma ƴan bijilante.
Hakan ya biyo bayan samun bayanan sirri ne da jami’an suka yi na ayyukan wasu ɓata-gari a wasu daga cikin unguwannin cikin birnin Kano.
A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Kwamishinan Labarai na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, abubuwan da aka ƙwato daga hannun ƴan dabar sun haɗa da ƙullin wasu ababe guda 283 da ɗaurin tabar wiwi 14, adda, almakasai uku da dai sauransu.
Sanarwar ta ce, tuni aka maka su a wata Kotun Shari’a da ke yankin Filin Jiragen sama na Malam Aminu Kano don su fuskanci hukuncin doka.
A ƙoƙarinsa na cigaba da wanzar da zaman lafiya da oda, kwamitin ya jaddada batun haramta yin tashe musamman la’akari da samun ayyukan dabanci acikin sa.
Haka kuma, an haramta buga banga a jihar, inda ya ce duk wanda aka kama, zai haɗu da fushin doka.
Shugaban kwamitin, Yusuf Ibrahim Ƙofar Mata, ya yaba wa ƙoƙarin jami’an wajen tabbatar bin umarnin hukumomi da na gwamnati acikin al’umma, ya na mai kira ga al’umma da su bada haɗin-kai wajen tabbatuwar zaman lafiya a jihar.