Ramadan: NSCIA ta buƙaci Musulmi su saurari ta bakin Sarkin Musulmi

Daga UMAR M. GOMBE

Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA) ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ta buƙaci al’ummar Nijeriya da su kasance cikin shiri don jin ta bakin Sarkin Musulmi kuma shugaban NSCIA na ƙasa dangane da soma azumin Ramadan na 1442 AH.

Cikin sanarwar da ta fitar a Lahadin da ta gabata ta hannun Daraktan Gudanarwa, Arc. Zubairu Haruna Usman-Ugwu, NSCIA ta buƙaci al’ummar Musulmi su zamo masu himma wajen gabatar da addu’o’i ga Allah musamman ma a watan Ramadan don alherin Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.

NSCIA ta ƙarfafa buƙatar neman watan Ramadan na bana da zarar rana ta faɗi a wannan Litinin, 12 ga Afrilun 2021 wanda ya yi daidai da 29 ga Sha’aban 1442 AH.

Da wannan majalisar ta buƙaci ɗaukacin Musulmin Nijeriya da su saurari sanarwar Shugaban NSCIA na ƙasa game da soma azumin na bana wanda za a bayar da yammacin wannan Litinin.

Majalisar ta kuma buƙaci Musulmi su zamo masu kulawa kan abin da ya shafi tsaro yayin Ramadan da kuma abin da ya shafi matakan kula da kafiya domin kare kai, masoya da kuma maƙwabta.

Sanarwar Majalisar ta zayyano mambobin Kwamitin Neman Wata na Ƙasa (NMSC) waɗanda ta ce ana iya tuntuɓar su game da sha’anin ganin watan Ramadan:

1 Sheikh Dahir [email protected]
2 Sheikh Karibullah Kabara [email protected]
3 Mal. Simwal Usman [email protected]
4 Sheikh Salihu Yaaqub [email protected]
5 Mal. Jafar [email protected]
6 Alh. Abdullahi [email protected]
7 Prof. J.M. [email protected]
8 Dr. Bashir Aliyu Umar 08036509363 [email protected]
9 Muhammad Rabiu [email protected]
10 Sheikh Abdur Rasheed [email protected]
11 Dr. Ganiy I. [email protected]@yahoo.co.uk
12 Gafar M. Kuforiji [email protected]
13 Prof. Usman [email protected]
14 Mal. Ibrahim Zubairu Salihu 08038522693 [email protected]
15 Dr. Usman Hayatu Dukku 0805 7041968 [email protected]
16 Imam ManuMuhammad 08036999841 [email protected]
17 Qadee Ahamad Bobboy 08035914285 [email protected]
18 Prof. Z. I. Oboh
Oseni 08033574431 [email protected]@gmail.com
19 Nurudeen Asunogie D. 08033533012 [email protected]
20 Sheikh Bala Lau 08037008805 08052426880 [email protected]
21 Sheikh Sani Yahaya Jingir 08065687545 [email protected]
22 Sheikh AbdurRahman Ahmad 08023141752 [email protected]
23 Muhammad Yaseen Qamarud-Deen 08055322087 [email protected]
24 Sheikh Lukman Abdallah 08052242252 [email protected]
25 Sheikh Sulaiman Gumi 08033139153 [email protected]
26 Sheikh Adam Idoko 08036759892 [email protected]
27 Alh. Yusuf Nwoha 08030966956 08026032997 [email protected]
28 Alh. AbdulBariu Kareem 09096369117 [email protected]
29 Prof. Kamil K. Oloso 08023098661 [email protected]
30 Malam Usman Mahmud 08034540120 [email protected]
31 Malam Yahaya Boyi 08030413634 [email protected]
32 Ustaz Mukail Abdurraheem 08099370109 [email protected]
33 Prof. Sambo Wali Junaidu 08037157100 [email protected]