Rana ta bace wa yan Boko Haram

Rundunar sojan Najeriya a jiya, ta yi nasarar dakile wani farmaki da mayakan Boko Haram su ka yi kokarin kaiwa garin Askira Uba.

Mai magana da yawun sojojin, Kanal Ado Isa, yace “Yan ta’addan Boko Haram, sun yi kokarin kawo hari garin Askira Uba a yau din nan, kuma sun yi wa garin kawanya ne ta kowacce shiyya, sai dai mayakan mu, sun samu galaba akan su”

Mayakan na rundunar Lafiya Dole, sun yi nasarar hallaka sama da yan Boko Haram 20, sun kuma kama makamai da dama. Cikin makaman da su ka kama sun hada da: Motoci dauke da manyan bindigogi guda 4, dama wasu da aka kona a yayin dauki ba dadin.

Haka kuma rundunar ta sojin Najeriya, ta kame wasu dadin makaman da suka hada da; Babura kirar Boxer guda 3, manyan bindigogi masu kakkabo jiragen sama guda 3, bindiga kirar AK47 guda 10, Gurneti guda 13, da kuma wasu harsasai masu yawan gaske.

Kanal Isa ya bayyana cewa a wannan fafutuka an kashe soji 1, kuma wasu guda biyu sun jikkata.

Sojojin Najeriya karkashin Janar Burtai, za su cigaba da wannan yaki, har sai sun ga karshen yan ta’adda a wannan yanki” In ji Kanal Ado Isa.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*