Ranar Dimokuraɗiyya: Akwai aiki babba a gaban Nijeriya – in ji Atiku

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa, akwai babban aiki a gaba kafin dimokuraɗiyyar Nijeriya ta samu cigaban da ya kamata.

Atiku ya bayyana haka ne a cikin saƙon Ranar Demokradiyya ta bana da ya isar wa ‘yan ƙasa a ranar Lahadi.

Ranar Dimokuraɗiyya rana ce da aka ƙayyade domin ‘yan ƙasa su duba su ga cigaban da aka samu a dimokuraɗiyyar ƙasa.

Wazirin Adamawa ya ce, kamata ya yi ‘yan Nijeriya da suka shaida mulkin soja a ƙasar su yaba da samun dimokuraɗiyya a matsayin tsarin mulkin ƙasa.

Ya bayyana a sanarwar da ya fitar cewa, dimokuraɗiyyar da za a yi ba tare da bin dokokin da aka shimfiɗa ba daga ɓangaren masu ruwa da tsaki ba, hakan zai zama babu wani bambanci da irin mulkin soja.

Ya ƙara da cewa, “kafin dimokuraɗiyyar ta samu irin cigaban da ya dace, dole a sauka daga tsarin da ake gudanar da ita a yanzu, inda masu riƙe da madafun iko ke ayya sakamakon zaɓe.”

Ya ce sau da yau idan ya zauna yana nazarin yadda ake tafiyar da dimokuraɗiyyar yau a ƙasar nan, sai ya ji ya ƙara haƙiƙance akwai babban aiki a gaban ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *