Ranar Dimukraɗiyya: Gwamnati na murna wasu na zanga-zanga

A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne Nijeriya ta yi bikin cika shekara 22 da komawar ƙasar kan turbar dimokuraɗiyya, inda mahukunta da `yan ƙasa suke ƙididdigar nasarori da kuma tarin ƙalubalen da ƙasar ta fuskanta da kuma wanda take kan fuskanta.

Wannan shi ne karon farko da ake bikin a wannan rana tun bayan sauya ranar bikin daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni da hukumomin ƙasar suka yi a shekarar da ta gabata, don tunawa da zaɓen MKO Abiola; Zaɓen da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin 1993 wanda a lokacin mutane suke ganin akwai yiwuwar Cif MKO Abiola zai iya lashe zaɓen, wanda kuma ana tsaka da zaɓen ne gwamnatin soji a lokacin ta yi amfani da kotu da ta bada izinin a dakatar da zaɓen.

Haƙiƙa wannan karramawa da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi wa dimokuraɗiyya da MKO Abiola karramawa ce ga duk wani mutum ɗan Nijeriya musamman waɗanda suka yi gwagwarmayar tabbatar da mulkin dimukuraɗiyya a ƙasar, ya nuna farin cikin sa akai.

To sai dai kuma ba a nan gizo ke saqa ba, domin bikin na bana kusan za a iya cewa ya zo ne a daidai lokacin da ƙasar take fama da ɗimbin matsalolin da sun zarce lissafin Ras-kwana, musamman na rashin tsaro da suka yi wa kowane yanki a ƙasar dabaibayi; a gefe guda kuma ga koma bayan tattalin arziki wanda ya saka ƙasar cikin tangal-tangal.

A maimakon al’ummar Nijeriya su cika da murna da yin shagulgula na kasancewar wannan rana kuma ta farko da aka fara yi tun bayan saka ranar a shekarar bara, sai kuma wasu ƙungiyoyi a jihohin Nijeriya suka cika wurare da zanga-zangar nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnati ke tafiyar da al’amuran ta, da kuma nuna ɓacin ran su da takaici akan yadda matsalar tsaro, satar mutane da yin garkuwa da su tare da kisan gilla da kai hare-haren da ‘yan bindiga ke yawan yi musamman a ƙauye da biranen arewacin qasar.

Ɗaruruwan masu zanga-zanga sun fito sun nuna cewa lallai gwagwarmaya ba ta ƙare ba, saboda wasu ƙungiyoyi sun cika biranen Ikko, Abuja da sauran biranen Nijeriya. Sannan an ga da dama daga cikin matasan da suka yi zanga-zangar suna kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya sauka mulki saboda abin da suka kira gazawar da gwamnatin sa ta APC ta nuna wajen tafiyar da al’amuran ƙasar yadda ya kamata.

A Abuja babban birnin tarayyar Nijeriya, rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun kai ruwa rana da jami’an tsaro, a lokacin da suka fara taruwa akan sha-tale-talen Gudu, amma daga baya `yan sanda sun tarwatsa su ta hanyar amfani da hayaƙi mai sa ƙwalla.

Wasu allunan da masu zanga-zangar suka riƙe na ɗauke da saƙonnin da ke cewa, “ `yancin faxin albarkacin baki, haƙƙin mu ne,” “A magance mana matsalar tsaro,” “Buhari ka sauka a mulki ka gaza” kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Haƙiƙa wannan zanga-zanga da ƙungiyoyin suka yi wani babban ƙalubale ne ga mulkin dimokuraɗiyya a Nijeriya, dalili kuwa shi ne, idan gwamnati ta tafi a haka, ta bar al’amura a rincaɓe, matsalar tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma suka gagari gwamnatin tarayya da na jihohi, to matasa za su iya mayar da ranar a matsayin ranar nuna ɓacin ransu da kuma nuna gazawar gwamnati muraratan a duk shekara, maimakon murnan ranar dimokuraɗiyya.

Babban abin kunya ne ga kowace gwamnati ta farar hula wadda talakawa suka sha rana suka zaɓe ta, a bayyana ta a matsayin wadda ta gaza faranta wa al’ummar ta rai a dimokuraɗiyyance, maimakon hakan sai duniya ta ga al’ummar ƙasar da suke tafiyar da mulkin dimukuraɗiyya suna kuka da gwamnati akan cewa ana masu mulkin danniya da kama-karya tare da tauye yancin faɗar baki da kuma rashin taɓukawa ko hoɓɓasa ta a-zo-a-gani kan daqile duk matsalolin da ke addabaryan ƙasa.

To ta yaya gwamnatin da ke kan tsarin dimokuraɗiyya musamman ta Shugaba Muhammadu Buhari za ta magance waɗannan matsaloli da ake ƙalubalantar ta? Ta hanyar shigewa kan gaba wajen yaƙar talauci da samar da ingantaccen ilimi ga yayan talakawa da yi masu kalaman sanyaya zuciya; hakan zai taimaka sosai wajen gyara tarbiyyar matasan mu da guje wa ruɗun ɓatagari masu zaman banza da shiga harkokin ta’addanci.

Gwamnatin ta samar da wata hanya sauƙaƙaƙƙiya ta bai wa matasa jari da tallafin kuɗi ko kayan sana’a ta yadda za su dogara da kan su a ɓangarori da dama, kama daga harkar noma da kiwo, bunƙasa hanyoyin fasaha da ƙere-ƙere da kuma ƙirƙiro da ƙananan sana’o’i domin matasa.

Kodayake gwamnatin APC ta yi ƙoƙari wajen rage raɗaɗin talauci ga yan Nijeriya, kamar yadda Shugaba Buhari ya faɗa a cikin jawabin sa na ranar dimokraɗiyya, inda ya ce gwamnatin sa ta fitar da mutum miliyan goma da rabi daga ƙangin talauci cikin shekara biyu da suka wuce. Wanda tun da farko da ma gwamnatin tasa tana da ƙudirin fitar dayan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin talauci cikin shekara goma duk da barazanar da annobar Korona ta yi wa tattalin arzikin ƙasa, a cewar sa.

Da irin wannan yunƙuri ne kawai matasa da dukkan al’ummar Nijeriya za su iya cin moriyar mulkin dimokuraɗiyya, da suka daɗe ba su amfana da shi ba. Saboda haka gwamnati ta tashi tsaye wajen tabbatar da muradun al’ummar ta, da daqile duk wani abun da zai harzuƙa talakawa su yi wa gwamnati bore a ranar da take gudanar da kowane irin biki. Maimakon murna sai a vige da kallon-kallo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *