Ranar Hausa Ta Duniya: Shin ko kwalliya ta biya kuɗin sabulu?

*Yadda aka gudanar da bikin a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Kaduna

Kasancewar bunƙasar harshen Hausa, wanda an yi ƙiyasin yana da masu amfani da shi kimanin mutane miliyan 50 a duniya, hakan ya sa ba tare da wani jeka-ka-dawo ba, Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ware duk ranar 26 ga Agusta a matsayin Ranar Hausa Ta Duniya.

Wannan dalili ne ya sa Taskar Nasaba tare da haɗin gwiwar Amale Hausa24, Ƙungiyar Matasan ‘Yan Jarida ta Jihar Kaduna da kuma sauran kafafen yaɗa labarai suka shirya wannan gagarumin taro a Kaduna, garin gwamna.

Wani sashe na mahalarta taro

Bikin, wanda aka gudanar da shi, don yin alfahari da inganta da kuma haɓaka harshen Hausa a duniya, an yi shi ne a cikin yanayi na ruwan sama.

Taron kuma ya gudana ne a ɗakin taro na Legacy da ke Gusau Institute a lamba biyu kan titin Dendo Road daura da titin Ahmadu Bello da ke garin Kaduna. 

Taron, wanda aka yi wa take da ‘Zaman Lafiya Da Ƙaunar Juna’, ya samu halartar malamai daga fannoni daban-daban na rayuwa, kama daga jami’o’i da tsangayoyin ilimi, da Kwalejin Kimiyya da Fasaha, da ‘yan siyasa da manyan baƙi, da kafafen yaɗa labarai, kamar Blueprint Manhaja, da ɗalibai da marubuta da manazarta daga cikin al’umma masu kishin harshen Hausa da masu ruwa da tsaki a fagen yaɗa Hausa da al’adunta.

Sannan akwai ƙungiyoyin gwamnati da masu zaman kansu da suke da nasaba da al’adun Hausa  musamman Ƙungiyar Marubuta ta Jihar Kaduna (MAJIK), da Ƙungiyar Jam’iyyar Matan Arewa, da kuma Gidauniyar (Women Support And Empowerment Foundation) duk su ma sun halarci wannan muhimmin taro. 

Daga ɓangare guda, akwai irinsu; Sheikh Halliru Abdullahi Maraya, da Farfesa Audee T Giwa, da Dakta Mu’azu Sa’adu Kudan, da Malam Lawal Musa Ɗanƙwari, da Malam Suleiman Mai Bazazzagiya, da Malam Ishaq Idris Guivi, da Malam Aliyu Umar, da Malam Rayyan Musa Lere, waɗanda suka gabatar da maƙaloli daban-daban.

Farfesa Hauwa Evylin

Kafin fara gudanar da taro kai-tsaye, kowa ya miƙe tsaye tare da sanya taken ƙasa (National Anthem) domin girmama wannan ƙasa ta Nijeriya.

Yayin da daga bisani aka ta fi izuwa maudu’i na gaba wato gabatar da kai. 

A farko, mai gabatar da jawabin taro ya umurci Salahuddeen Muhammad, Shugaban Taskar Nasaba da ya bayyana manufofinta, in da ya yi bayani kamar haka; 

A cewarsa: “Taskar Nasaba muryar gaskiya ce game da nahiyar Afirka, murya ce don maido da tarihi da al’adu na ainihi. Manufar ita ce, gina nagartattun tsari ta hanyar bunƙasa al’adu, da tarihi da kuma yawon buɗe ido, don maido da hanyoyi na gaskiya, tunani da salon rayuwa.”

Ya cigaba da cewa, “Taskar Nasaba, ta wanzu ne don sake duba labaran Afirka don taskancewa, fassarawa, baddalawa, warkarwa, sabuntawa da sake fasali ta hanyar zamani. Ta kuma kasance ne don tunatarwa da ƙarfafa gwiwa, domin gyara labaran ƙarya da haifar da bege da canji ga makomar Afirka.

“Mun ƙudiri aniyar ɗaga muryoyinmu domin ganin martabar Afirka ta dawo, kuma ta hanyar yin hakan za mu iya canja yadda muke ji ko gani game da Afirka a yau.

“Lokaci ya yi da ma fi kyawun nahiyar Afirka zai bayyana, kuma da za a yi imani da rayuwa. Haka nan, lokaci ya yi da za mu nuna martabobinmu da kuma bunƙasa su,” inji shi.

Bugu da ƙari, a lokacin bikin an samu nasarar gabatar da maƙaloli ɗaya bayan ɗaya har guda takwas waɗanda suka haɗar da: “Nishaɗi, zamantakewa da zaman lafiya a cikin wasu daga cikin waƙoƙin Dr. Mamman Shata,” wacce Farfesa Audee T. Giwa ya gabatar. “Kura Sha Zagi” wanda ta zo daga bakin Dakta Mu’azu Sa’adu Kudan. Sai waƙar “Ranar Hausa” da Malam Suleiman Mai Bazazzagiya ya rera. Sai maƙala ta gaba wato “Harshen Ingilishi: Ga ƙoshi ga kwanan yunwa” daga bakin Malam Ishaq Idris Guivi. 

Mal Sula’eiman Mai Bazazzagiya

Sauran waɗanda suka gabatar da maqalolin akwai: Malam Lawal Musa Ɗanƙwari da ya yi jawabi a kan “Tasirin Harshen Hausa A Duniya.” Sai kuma Malam Aliyu Umar da ya kalli tasirin “Hausawa Da Maƙwabtansu.” Sai takarda ta ƙarshe da Malam Rayyan Musa Lere ya yi mata take da “Gudunmawar Gidajen Rediyo Wajen Bunƙasar Harshen Hausa.”

Sai Sheikh Dakta Halliru Abdullahi Maraya, wanda shi ma ya gabatar da maƙala a kan taken taron na bana wato “Zaman Lafiya Da Ƙaunar Juna.”

Shi ma a nasa jawabin Farfesa Audee T. Giwa ya yi kira ga al’ummar Hausawa da su dinga komawa ga ɗabi’ar Malam Bahaushe ta asali wadda take cike da tawakkali da kuma tauhidi, in da ya kawo misalai da dama a kan waƙoƙin Marigayi Dakta Mamman Shata Katsina a waƙarsa ta “Na tsaya ga Annabi Muhammadu” da kuma “Don sallah da salatil fatih don Allah mata ku yi aure.”

Har ila yau, an yi kira ga mahauta da su daina sanya sunan “Suya Spot” a rubutunsu na wurin sana’a maimakon haka su mayar da shi “Tukuba” kasancewar sana’ar ta fawa sana’a ce ta Malam Bahaushe tun asali.

A fagen nishaɗantarwa kuwa; Ya’u mai Kalangu ne ya motsa zukatan jama’a ta hanyar yin kiɗan taushi. A nasa vangaren, shi ma ba a bar Abubakar Mai Bibbiyu a baya ba wajen rera wata sabuwar waƙarsa mai taken “Da’irar Mawaƙa” yayin da ya shigo bainar jama’a. 

Har ila yau, wasu daga cikin manyan baƙi irinsu; Farfesa Hauwa Evelyn Yusuf, da Hajiya Asma’u Yawo Halilu (Shugabar Ƙungiyar ‘Yan Jaridu ta Ƙasa, reshen Jihar Kaduna), da Malam Ɗahiru Ahmad (Mataimakin Shugaban Gidan Rediyo da Talabijin na Liberty Kaduna), da Hon. Musa Zamzam, da Hon H. E Hayatuddeen (Ɗan takarar Gwamnan Jihar Kaduna a Jam’iyyar PRP), da Hajiya Ɗaharatu wacce ta wakilci Hajiya Rabi Musa Saulawa (Shugabar Ƙungiyar Jam’iyyar Matan Arewa), da Hajiya Falmata Abacha cna (Shugabar Gidauniyar Women Support And Empowerment Foundation) da kuma Malam Aliyu Tahir wanda ya wakilci Umar Faruq Musa (Shugaban Rukunin Kamfanin Vision Media Limited, Jabi, FCT-Abuja), duk sun nuna jin daɗin da kasancewa a irin wannan farfajiya tare kuma da jaddada bada tasu gudunmawa wajen haɓaka harshen Hausa. 

Taron bai yi togaciya a nan ba, ya ƙara wa daɓensa makuba ta hanyar raba kyaututtukan karramawa ga waɗanda suke bada gagarumar gudunmawa wajen inganta harshen Hausa. 

A ƙarshe an karrama wasu zaƙaƙuran mutane da suke bayar da gudummuwa ta fannoni daban-daban a cikin al’umma. Waɗanda aka karrama ɗin sun haɗa da: Alhaji Najib Mustapha Bawa Tsafe na Liberty Rediyo/TV Kaduna da Hon. Musa Zamzam (Shugaban Kamfanin gidan biredin zamzam da Malam Adamu Mustapha (Sardaunan Daitu, Shugaban kamfanin Sardauna Strategy Global Ventures); da Malam Tanko Rossi Sabo (Jagaban Ayu); da Falmata Abacha cna (Shugabar Gidauniyar Ideal Women Support And Empowerment Foundation); da Alhaji Ibrahim Mohammed T (Shugaban Tawad Press) da Yunusa Ibrahim AMNIM, MCILRM, MICA (Malami a sashen koyar da lissafi ta Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Kaduna) da Hajiya Rabi Musa Saulawa (Shugabar Ƙungiyar Jam’iyyar Matan Arewa).

Sauran su ne: Malam Ɗahiru Ahmad (Mataimakin Shugaban Gidan Rediyo da Talabijin na Liberty Kaduna) da Umar Faruq Musa (Shugaban rukunin kamfanin Vision Media Limited, Jabi – Abuja) da Alhaji Falalu Ɗalhatu (Zannan Zazzau).

Daga ƙarshe, Shugaban Taskar Nasaba, Malam Salahuddeen Muhammad, wanda kuma shi ne Shugaban Taron, ya miƙa saƙon godiya da bangajiya ga ɗaukacin waɗanda suka halarci taron musamman manyan malamai da manyan baƙi, da marubuta, da manazarta, da ɗalibai, da kuma kafofin yaɗa labarai irinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *