Ranar Hijabi: Ɗalibai suna da ‘yancin sanya hijabi a makarantu – Gwamna Makinde

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo a ranar Talata ta makon jiya ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnatinsa ba za ta take musu haƙƙinsu na addini ba.

Makinde ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin addinin Musulunci, Abdulrasheed Abdulazeez, ya fitar domin bikin ranar Hijabi ta duniya ta 2022.

“Hijabi sutura ce da ba wai kawai tana ƙawata mai sakawa ba, har ma tana taimakawa wajen ci gaban ɗa’a a cikin al’umma,” inji Makinde.

Gwamnan ya taya al’ummar musulmin jihar murna musamman mata, ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatinsa ba za ta soki duk wasu ɗabi’u da za su inganta ibada da kunya ba.

“Ɗalibai musulmi da suke son sanya hijabi a makarantun gwamnati a jihar Oyo ba a tauye musu haƙƙinsu ba,” in ji shi.

“Na umurci masu riƙe da muqamai a ma’aikatan gwamnati da kuma ɗaukacin makarantun gwamnati da kada su tursasa kowa ko musguna wa wani saboda addininsa ko kuma ayyukansa.

“Gwamnatinmu mai tsoron Allah ce, kuma za mu ci gaba da wa’azin juriya na addini, daidaito da adalci, wanda zai ƙara samar da zaman lafiya da soyayya da haɗin kai.

“Kamar yadda taken bikin na bana ya nuna, hijabi abin alfahari ne ga kowace mace musulma kuma ya kasance mai tsarki,” inji shi.

Makinde ya kuma yi kira ga shuwagabannin addinai daban-daban da su riƙa haɗa kai da gwamnatin jihar kan kowane irin lamari domin kauce wa rikicin addini.