Ranar Jini ta Duniya: ‘Yan Afirka milyan 7 ke buƙatar jini duk shekara – WHO

Daga UMAR M. GOMBE

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya (WHO), ta ce a shekarar da ta gabata an samu koma baya dangane da gudunmawar jini da ake samu a yankin Afirka saboda cutar korona.

WHO ta ce mutane ‘yan ƙalilan ne aka samu suna ba da gudunmawar jini sakamakon ɓullar annobar korona.

Daraktar Shiyya ta WHO a Afirka, Dr Matshidiso Moeti, ta ce ƙarancin gudunmawar jini da ake fuskanta na da nasaba da hana tafiye-tafiye da aka yi don cutar korona da kuma tsoron harbuwa da cuta su ne suka hana mutane ziyartar cibiyon ba da gudunmawar jini.

Ta ce, “Akwai kimanin mutane milyan bakwai a Afirka da ke buƙatar gudunmawar jini don ceto rayuwarsu duk shekara.”

A cewarta, ana bikin Ranar Jini ta Duniya ne a ranar 14 ga watan Yunin kowace shekara, yayin da taken bikin 2021 ya kasance: “Ba da gudunmawar jini don raya duniya”.

Ta ci gaba da cewa, jini mai tsafta da kuma ba da shi ababe ne masu muhimmanci wajen ba da cikakken kula da lafiya da ceto rayuwar mata da ‘ya’ya a lokacin haihuwa.

Kazalika, ta ce ana buƙatar jini wajen yi wa mutane fiɗa da kuma magance cututtuka masu alaƙa da jini da sauransu. Tare da da cewa ana ajiyar jini ne na taƙaitaccen lokaci, don haka ana buƙatar gudunmawar jini mara yankewa don cimma biyan buƙata a duk lokacin da buƙatar jini ta taso.