Ranar Litinin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai dawo da aiki – Gwamnati

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta sanar da Litinin mai zuwa a matsayin ranar da za a dawo da zirga-zirgar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna.

Kakakin Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Nijeriya (NRC), Yakub Mahmoud ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Asabar.

Ya ce, gabanin dawo da sufurin a ranar ta Litinin, hukumar za ta fitar da cikakkun bayanai ga jama’a ranar Lahadi.

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ne Ministan Sufurin Jiragen Ƙasa na Nijeriya, Mu’azu Jaji Sambo, ya sanar da cewa kafin ƙarshen watan Nuwamban 2022 za a dawo da sufurin bayan shafe wata takwas da dakatar da shi.

Ministan dai ya ce za a dawo da sufurin ne kawai idan aka tabbatar da samar da isasshen tsaro a titunansa.

Ya ce, dole a tabbatar da ɗaukar wasu matakan tsaro kafin a kai ga dawo da sufurin, wanda ya haɗa da samar da na’urorin da za su riƙa sa’ido a kan kaiwa da komowar jirgin.

An dai dakatar da sufurin ne a watan Maris ɗin da ya gabata, lokacin da ’yan ta’adda suka kai masa hari, inda suka kashe wasu fasinjojin suka kuma yi garkuwa da wasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *