Ranar littafi ta duniya: Adadin litattafan da Sinawan suka karanta ya ƙaru a 2021

Daga CMG HAUSA

Cibiyar nazarin dab’in labarai ta ƙasar Sin ta fitar da sakamakon binciken da aka yi game da karanta litattafai na al’ummun Sinawa karo na 19 a yayin babban taron karanta litattafai karo na farko da aka shirya da yammacin yau Asabar 23 ga wata, inda aka bayyana cewa, adadin litattafan da kowanen Sinawan da suka kai shekarun haihuwa 18 ya karanta a shekara 2021 ya kai guda 4.76, adadin litattafan da ya karanta ta yanar gizo ya kai guda 3.3, duka sun karu bisa na shekarar 2020.

Kana adadin litattafan da kowanen Sinawa waɗanda ba su kai shekarun haihuwa 17 ba ya karanta ya kai guda 10.93, adadin da ya ƙaru da 0.22, idan aka kwatanta da shekarar 2020.

Shugaban ƙasar Xi Jinping ya aike wa babban taron wasiƙar taya murna, inda ya bayyana cewa, yana fatan daukacin al’ummun Sinawa za su kara nuna kuzari kan karanta litattafai.

Mai fassarawa: Jamila