Ranar Malaria ta duniya: ga yadda ƙwararrun Sin ke taimakawa Sao Tome da Principe yaƙi da Malaria

Daga CMG HAUSA

Ranar 25 ga watan Afrilu rana ce ta yaki da cutar Malaria ta ƙasa da ƙasa. Guo Wenfeng, wani ƙwararren likita ne daga tawagar ƙwararrun masu bada agajin kiwon lafiya ta ƙasar Sin dake yaki da zazzabin cizon sauro wato malariya a tsibirin Sao Tome da Principe, ya bayyana yadda suke gudanar da aikinsu na yaƙi da cutar malariya a wannan yanki.

Yaƙi da cutar malariya ya kasance ɗaya daga cikin muhimman ɓangarorin kiwon lafiya na haɗin gwiwa a tsakanin ƙasashen Sin da Sao Tome da Principe.

Idan aka yi la’akari da irin nasarorin da aka cimma a halin yanzu, kuma idan aka kwatanta da haƙiƙanin yanayin da ake ciki a tsibirin São Tomé da Príncipe, ƙasar Sin ta taimakawa São Tomé da Príncipe wajen tsara sabbin dabarun yaƙi da malariya waɗanda suka fi mayar da hankali wajen dora dukkan mutane kan amfani da magunguna, gami da wasu dabarun daƙile hayayyafar sauro, matakan sun haifar da muhimman sakamako a ƙauyuka da dama da cutar malariya ta yi ƙamari.

Domin ƙara faɗaɗa sakamakon da aka samu na yaƙi da cutar malariyar, bayan haɗin gwiwa da ma’aikatar kiwon lafiyar São Tomé da Príncipe, tagawar ƙasar Sin dake yaƙi da cutar malariyar, za ta gudanar da aikin gangamin rabon magunguna na ƙasa baki ɗaya a wasu ƙauyuka 10 inda matsalar cutar malariyar ta fi tsanani, a shiyyar Agua Grande tsakanin watan Maris zuwa watan Yunin wannan shekarar.

Guo Wenfeng ya yi amanna cewa, ta hanyar haɗin gwiwar ƙut-da-ƙut tsakanin tawagogin yaƙi da cutar malariyar na Sin da Sao Tome da Principe, shirin zai yi matuƙar tasiri wajen rage girman matsalar cutar malaria, kuma zai inganta rayuwar mazauna wurin, kana zai taimakawa tsibirin Sao Tome da Principe wajen cimma nasarar muradun kawar da cutar malariya baki ɗaya nan da shekarar 2025.

Mai Fassara: Ahmad