Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Cibiyar fasahar sadarwa da cigaban al’umma (CITAD) ta yi bikin ranar tunawa da masu buƙata ta musamman da ake gudanarwa duk ranar 3 ga watan Disambar kowace shekara, da ya gudana yau a cibiyar CITAD da ke Kano.
Shugaban Cibiyar Fasahar sadarwa da cigaban al’umma ta CITAD wanda jami’in shirye-shirye na Cibiyar, Mal. Isah Garba ya wakilta ya bayyana cewa, muhimmancin ranar ne ya sa CITAD ta shirya taron domin tattauna matsalolin matune masu buƙata ta musamman da kuma shawarwari akan yadda za a magance matsalolin na su.
“CITAD ba wai kawai mun shirya taron a rana ɗaya ba ne kawai a’a mun shigar da masu buƙata ta musamman cikin dukkan ayyukanmu na yau da kullum”
Ya ƙara da cewa” Wannan ne ya sa a matsayinmu na ƙungiya mai zaman kanta da ta ke da manufa akan yaɗa ilimin fasahar sadarwa ya zamana cewa mun ware ɗakin koyar da karatu na bada horon kwamfiyuta ga su waɗannan masu buƙata ta musamman, saboda ko ba komai a yadda duniya take tafiya matuƙar ba ka da ilimin kwamfiyuta to an barka a baya a dukkanin fannonin rayuwa wannan ne ya sa muka samar da wannan”
Ya cigaba da cewa, ina kira ga gwamnatoci da ta tabbatar da cewa duk wani abu da za’a yi a tabbatar an shigar da masu buƙata ta musamman, an saurari muryoyinsu an kuma ji menene buƙatunsu, kada mu ƙaddara cewa kaza da kaza ne matsalarsu, a’a su suka san matsalarsu su Kuma ya kamata su faɗi matsalarsu. Kuma da su ya kamata mu yi aiki mu tabbatar”
Su kuma al’umma su gane cewar waɗannan mutane, mutane ne kamar su suka samu wata matsala tun farkon rayuwarsu ko kuma ƙarshen rayuwarsu, kuma babu wani mutum da ya wuce wannan matsala ta same shi a matsayinsa na ɗan Adam, don haka mu ja su a jiki mu shigar da su cikin al’umma, kuma Allah ya zuba baiwa a cikin waɗannan al’umma ,tabbas za su iya warware mana wasu matsaloli da suka damemu”. Inji Isah Garba
Hamza Aminu Fagge shi ne jami’in kula da masu buƙata ta musamman na CITAD ya bayyana cewa suna cikin farin ciki da murnar ta wannan rana, domin yace sun haɗu da yan’uwa da aka daɗe ba a haɗu ba, ga Kuma ƙaruwa da lakcoci da aka yi a wurin.
Sannan ya yi kira da masu buƙata ta musamman da su zage damtse wajen neman Ilimi ta yadda su ma za a dama da su, kuma a shigar da su cikin kowane fanni na rayuwa.
Taron na bana ya samu halartar manyan malamai daga jami’oi da masana, da su kansu masu buƙata ta musamman daga unguwanni daban- daban na Jihar Kano.