Ranar Mata: Ƙungiya ta horar da mata 100 girki a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ƙungiyar Northern Chef Kamal Foundation ta horar da mata guda 100 dabarub girke-girke daban-daban, saboda ƙaratowar azumi, da ya  gudana a ranar Laraba a Unguwar Hotoro dake Kano, inda taron ya zo daidai da Ranar Mata ta Duniya.

Da yake jawabi a wajen, shugaban ƙungiyar kuma wanda ya ƙirƙiri ƙungiyar Chef Kamal Ahmad ya ce ƙungiyar ta shirya taron ne domin horar da mata 100 da kuma murnar zagayowar ranar mata ta duniya.

Ya ce babban maƙasudin horarswar shi ne samar da ingantaccen abinci mai gina jiki musamman a wannan wata na azumin Ramadan da ke ƙaratowa, da kuma ƙara ƙulla kyakkyawar alaqa a tsakanin ma’aurata da bai wa yara abinci mai inganci.

Baya ga koyar da abinci ƙungiyar Northern Cheef tana ciyarwa da raba dafaffen abinci ga mabuƙata, da kuma ciyar wa a lokacin azumi, ya kuma ce a cikin shekaru 3 da kafa ƙungiyar sun  horar da mata fiye da 500 girki a Jihar Kano.

Sannan ya yi kira da al’umma da kuma gwamnati wajen tallafa wa irin wannan ƙungiya don ɗorewar wannan aiki na alheri don sanya farin ciki a zukatan al’umma.

Taron dai ya samu halartar mambobin ƙungiya na ƙananan hukumomin daban-daban na Kano.