
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan-adam ta Amnesty International a Nijeriya dake Jihar Ogun, ta yi kira ga masu-ruwa-da-tsaki da su yi aiki wajen dakatar da yawaitar kisan mata a ƙasar.
Kodinetan ƙungiyar na jihar, Joshua Oyebode ya bayyana hakan a yayin wani gangamin wayar da kan al’umma da zagayen murnar ranar mata ta duniya.
An ga mutane da dama a dandazon jama’ar sanye da rigunan da ke ɗauke da rubutun ‘Stop Femicide’, wato a dakatar da kashe mata, a Oshogbo, Babban Birnin jihar.
Ya koka ga yadda ake yawan samun hatsaniyar da ke haddasa mutuwar mata , inda ya a ce, a shekarar 2024 kaɗai kimanin mata 149 ne aka kashe a Nijeriya.
Oyebode ya ce, sun yi gangamin ne don nuna illar da ire-iren hakan ke haifarwa acikin al’umma, ya na mai cewa lallai sai masu-ruwa-da-tsaki sun haɗu wajen samar da hanyoyin dakatar da hakan da ake yi babu gaira babu dalili a ƙasar.
Ya kuma bada misali da rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya kan ƙwayoyi da manya laifuka, wanda ya ce akan samu mata da ƴan mata 140 da ake kashewa a kullum a faɗin duniya, ya na mai kira ga masu-ruwa-da-tsaki da su bai wa ɓangaren muhimmanci wajen shawo kan matsalolin da ke haifarwa.