Ranar ‘Yan Mazan Jiya: Gwamnan Zamfara ya sha alwashin tallafa wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta cigaba da ƙoƙarin inganta rayukan iyalan jami’an sojojin da suka rasa rayukansu a bakin aiki.

A lokacin da ya ke jawabi a taron ranar tunawa da ƴan mazan jiya ta 2025 a filin taro na Trade Fair dake Gusau, gwamnan ya sanar da bada tallafin Naira miliyan 20 ga iyalan sojojin na reshen jihar Zamfara.

Kakakinsa, Sulaiman Bala Idris kamar yadda ya bayyana a wata takarda, ya ce gwamnan ya gabatar da tallafin ne a lokacin da ya ke ƙaddamar da buɗe taron na shekarar 2025 da aka gudanar a ranar Laraba.

Gwamnan ya ce, ranar lokacin ne na nuna godiya da jinjina ga jami’an da suka rasa rayukan nasu da kuma kira ga al’ummar jihar da su ɗauki mataki da ma ƙasar baki ɗaya.

A kowacce ranar 15 ga watan Junairu ake bikin tunawa da sojojin kan irin muhimmiyar rawa da suka taka wajen bai wa ƙasa da al’ummarta tsaro.

Gwamna Dauda Lawal ya kuma ce “Mun yaba da daraja ƙoƙarinsu da sadaukarwa waɗanda suka samar da sauyi a rayukanmu a yau. Tare da godiya da himma, mun ƙudiri aniyar cigaba da tunawa da su da taimaka wa makusantan da suka bari.”

Ya ƙara da cewa, duk da ƙarancin kayan aiki, ana samun nasara wajen magance matsalolin tsaro ta ɗaukar matakai da dama.