Ranar Zaman Lafiya ta 2022: A kiyaye ’yanci da haƙƙoƙin juna

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Tun a shekarar 1981 ne Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da tsayar da ranar 21 ga watan Satumba na kowacce shekara domin ta zama ranar da duniya za ta mayar da hankali wajen tattauna muhimman batutuwan da za su ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummomi daban-daban. Yayin da a kowacce shekara ake zaɓar wani darasi da za a yi nazari a kansa, saboda tasirin sa da muhimmancinsa kan ga al’amarin zaman lafiya.

A bana bikin ranar ya duba yadda za a kawar da batun nuna wariyar launin fata da inganta zaman lafiya. Ko da ya ke, mu a nan Afirka tun a shekarar 1990 aka kawo ƙarshen nuna wariyar launin fata a ƙasar Afirka ta Kudu wata ni biyu bayan samun ‘yancin kan ƙasar Namibiya, ƙasa ɗaya da ta rage ana nuna baƙin mulki kwatankwacin na mulkin mallaka, inda baƙaƙen fata ‘yan asalin ƙasar suke rayuwa cikin ƙangi da nuna danniya da zaluncin gwamnatin fararen fata da suka riƙa bautar da su suna mayar da su ƙasƙantattu a cikin ƙasar su ta haihuwa.

Ko da ya ke har kawo yanzu a ƙasashen Turai inda suke da ‘yan ƙasa baƙaƙen fata ana cigaba da fuskantar ƙalubalen wariya da ƙyamar baƙaƙe da wasu tsiraru masu jajayen fata, duk kuwa da kurar in da suke yi na yaƙi da wariya da ‘yancin da kowanne irin launin mutum ya ke da shi a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin ƙasashensu, ko dokokin ƙasashen duniya.

Idan muka koma ga taken bikin ranar da yadda ya shafi yankin mu na Afirka ko ƙasar mu Nijeriya musamman, za mu ga ko da babu wariyar launin fata a tsakanin mu, amma akwai nuna wariyar addini da ƙabilanci ko ɓangaranci, duk da yake kundin tsarin mulkin ƙasa a babi na huɗu sashi na 41 an bai wa kowanne ɗan ƙasa ‘yancin ya shiga ko’ina a Nijeriya, kuma ya zauna a duk inda ya ga dama ba tare da tsangwama ko kora ba.

Amma abin mamaki a cikin Nijeriya ma sai ka ga wani bashi da ‘yancin samun sauƙin rayuwa ko walwala kamar sauran ‘yan jiha, sai a riqa nuna masa wariya da sunan shi ba asalin ɗan jihar ba ne. Saboda kakanin kakaninsa ba ‘yan asalin nan jihar ba ne, saboda irin sunansa, addininsa ko harshensa.

A wata jiha a cikin Nijeriya ‘yan wata ƙabilar ba su da ‘yancin shiga takarar neman zaɓe a wasu muƙamai kamar irin su Gwamna ko Sanata, saboda su tsiraru ne ba su da yawa, ko da kuwa sun fi saura gogewa da cancanta. A Jihar Filato, da ke yankin Arewa ta Tsakiya, Musulmi mazauna jihar na kokawa da halin wariya da tsangwama da suke fuskanta a matsayin su na ‘yan asalin jihar ko matsayin su na ‘yan ƙasa. Duk kuwa da yawan da suke da shi a jihar, amma ba su da ‘yancin neman takarar neman kujerar Gwamna, ko samun Mataimakin Gwamna, Ko Kakakin Majalisar Jiha. ’Ya’yan su ba su da ‘yancin samun tallafin karatu ko na lafiya kamar sauran yara, saboda iyayensu suna Sallah.

Hatta a wurin ɗaukar aiki Musulmi ƙalilan ne suke samun damar a ɗauke su a aiki, su ɗin ma sai in sun fito ne daga wasu ƙananan hukumomin jihar irin su Wase, Kanam, da Mangu. Su ɗin ma ba sa jin daɗin mu’amalar da ake nuna musu, musamman a abin da ya shafi aikin gwamnati da sauran abubuwan da suka shafi hukuma.

Za mu ga irin haka a yanayin yadda muke mu’amala a tsakanin mu, ‘yan gari ɗaya, ko ƙabila ɗaya, hatta a addini ɗaya ma bambancin aƙida, mazhaba, ƙungiya ko majami’a shi ma yana sa ka ga ana nuna wa wani ƙiyayya da ƙyama, don fahimtarsa ta addini ta bambanta da ta sauran mutane.

Dubi dai yadda muke nuna ƙyama ga mabiya aƙidar Shi’a, da nuna bambanci tsakanin ‘yan Izala da ‘yan ɗariƙa. Haka abin ya ke ma ɓangaren mabiya addinin Kirista, bambancin ɗariƙa ko majami’ar da mutum ke zuwa ya isa a hana shi aure ko aiki, ballantana a mutunta shi.

’Yan Arewa da ke zuwa yankin kudancin ƙasar nan, da sunan aiki, kasuwanci ko wata sana’a, su ma suna ganin tsanani da halin ƙuntatawa don kawai sun fito daga yankin Arewa. Kwanaki mun ga irin yadda aka riqa farautar rayuwarsu a jihohin Kudu maso Gabas inda ‘yan ƙabilar Ibo suka fi rinjaye, saboda kawai ɗan uwansu ne ke shugabancin ƙasa, ko suna amsa sunan Musulunci.

Tsirarun ƙabilu da ke wasu jihohin Arewa su ma haka suke ƙorafi a wasu wurare, sakamakon wariyar da suke zargin ana nuna musu, saboda suna bin addinin Kirista ko kuma don su ba Hausawa ba ne. Alaƙar Talakawa da masu kuɗi ma haka ta ke, kullum tazarar da ke tsakanin su ƙara nisa ta ke yi, musamman a ɓangaren zamantakewa, karatu, asibitoci, da kasuwanci, komai na talaka a wulaƙance ya ke, babu kulawa ko gyara.

Muddin muna son a samu ingantaccen zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummomin da ke ƙasar nan da ma duniya baki ɗaya to, tilas ne sai an kawar da wariya da nuna ƙyamar wani ɓangaren al’umma, saboda bambancin su da wasu ko kuma ƙarancinsu. A ilimantar da jama’a sanin muhimmancin haƙƙoƙin juna kamar yadda ya ke a koyarwar addinan mu da kuma kundin haƙƙoƙi na Majalisar Ɗinkin Duniya, domin a samu zumunci mai ƙarfi da mutunta juna.

Yadda Ubangiji Ya halicci mutum ko ‘yan Adam ya yi su da launi iri-iri, ƙabila, ko fahimta daban-daban, wanda hakan kuma sai ya mayar da duniyar ta zama abin sha’awa. Sai dai yadda muke kallon wasu a matsayin masu fifiko wasu kuma masu ƙasƙanci ya sa duniyar ta yi mana wuyar zama. Mun kasa zama waje ɗaya mu fuskanci junanmu, da batutuwan da za su kawo mana cigaba, rabuwar kai da wariya ta hana mana samun ƙarfin da za mu gina kanmu.

Babu shakka nuna wa juna ƙyama ko ƙasƙanci babbar damuwa ce a zaman tare. Babu wanda ya ke so a yi masa kallon wulaƙanci, ko a nuna ba shi da daraja ko wata martaba da za a saurare shi ko a biya masa buqata. Ko ɗan da mutum ya haifa ne yana haƙƙoƙin da ya kamata ka kiyaye masa, a matsayin ka na uba ko uwa, domin ku ma ku samu ladabi da biyayyar da ku ke nema daga wajensa.

Zaman lafiya an ce ya fi zama ɗan sarki. Hankalin mu ba zai tava kwanciya ba, burin mu ba zai taɓa samuwa ba, arziƙin mu da cigaban ƙasashen mu da yankunan mu ba za su samu ba, sai mun mutunta juna da kare haƙƙoƙin junanmu. Mu daina nuna wa juna wariya da danniya in muna son mu ga daidai!