Rasha ta fara ƙaddamar da farmaki kan Ukraine

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya sanar da ƙaddamar da ayyukan soji a kan Ƙasar Ukraine bayan share tsawon makwanni ana zaman tankiya da kuma gazawar matakai na diflomasiyya tsakanin Rasha da ƙasashen Yammacin Duniya.

Shugaba Putin ya sanar da ƙaddamar da farmakin yayin wani jawabin ba zata da ya gabatar a gidan talibiji da misalin ƙarfe shida na safiyar yau agogon Rasha, inda ya buƙaci dakarun Ukraine su gaggauta ajiye makamansu musamman a yankunan da ke gabashin ƙasar ta Ukirane.

Putin, ya ce, ya ɗauki wannan mataki ne domin kauce wa faruwar kisan kiyashin da mahukuntan birnin Kiev suka tsara aiwatarwa a yankin tare da kawo warshen take-take irin na tsoƙana da ƙasashe mambobi a ƙungiyar NATO ke yi wa Rasha.

Ministan tsaron ƙasar ta Ukraine Dmytro Kouleba, ya ce, Rasha ta tsara gagarumin shirin mamaye ƙasar, kuma tun a sanyin safiyar yau ta fara kai hare-hare da kuma jin ƙarar fashewar abubuwa a wasu biranen ƙasar ciki har da birnin Kiev. Tuni dai Ukraine ta sanar da rufe sararin samaniyarta ga jiragen da ke jigilar fasinja.

Babban Magatakardar Majalisar Xinkin Duniya Antonio Guterres, ya buƙaci tsagaita wuta a cikin gaggauwa, sai kuma shugaba Joe Biden na Amurka wanda ya yi tir da wannan farmaki na Rasha yayin da ƙungiyar tsaro ta NATO ke shirin gudanar da taron gaggawa kan lamarin a yau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *