Rashin aiki ga matasa ne silar matsalar tsaron Nijeriya, cewar Atiku

Daga FATUHU MUSTAPH

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya danganta matsalar tsaron Nijeriya da rashin aikin yi ga matasa, inji wata sanarwa da Waziri Adamawa ya fitar a Lahadin da ta gabata.

Atiku ya ce bai taɓa jin wata damuwa ba da faɗin abin da shi ne daidai. Yana mai cewa duba da rahoton da Bloomberg Business ta fitar a Asabar da ta gabata, cewa Nijeriya za ta zama ƙasar da ta fi kowace yawan marasa aiki a faɗin duniya inda yanzu adadin narasa aikin ya kai kashi 33 cikin 100.

“Wai yaya aka yi Nijeriya ta kai ga haka? Mun kai wannan matsayi ne sakamakon sakaci da salon shugabanci da rashin bada damar gudanar da kasuwanci a sake da rashin aiwatar da wasu tsare-tsare tun na zamanin mulkin Obasanjo….”, inji Atiku.

Ya ƙara da cewa, “Duk da kuɗaɗen da gwamnati ke da su, mun ci gaba da saka gwamnati cikin harkokin da suka kamata ‘yan kasuwa ne ke jan ragamarsu, wanda ƙarami daga ciki shi ne batun kuɗi Dala bilyan $1.5 da aka ware domin gyaran matatar mai ta Fatakwal wanda haƙa ta kasa cim ma ruwa a shekaru.

“Abin da ya kamata wannan gwamnatin ta sani shi ne, matsalar tsaron da Nijeriya ke fuskanta hakan na faruwa ne sakamakon rashin aiki ga matasa.

” Zaman kashe wando shi ne abu mafi muni game da abin da ya shafi rashin aiki saboda hakan na hana cin moriya matasan wajen gina ƙasa face su zama masu lalata ƙasa, wanda hakan shi ne dalilin da ya sa a yau Nijeriya ta zama ƙasa ta uku da ta fi fama da matasalar ta’addanci a doron ƙasa.

“A 2020, na bada shawarar kan cewa domin karya lagon matsalar rashin aiki a ƙasar nan, duk iyalin da akwai yaron da ya isa zuwa makaranta kuma yake samun ƙasa da Dala $800 a shekara, a bai wa iyalin tallafin kuɗi N5000 duk wata daga aljihun gwamnati ta hanyar amfani da lambar BVN da NIN a bisa sharaɗin za a bai wa karatun yaro muhimmanci.

“Har yanzu dai ina kan bakana dangane da wannan shawarar da na bayar, musamman a irin wannan lokaci da ake fuskantar matsalar rashin aiki a tsakanin matasa.

“Muddin za mu kula da karatun yara milyan 13.5 da ba su zuwa makaranta a faɗin Nijeriya, za a iya cin galabar matsalar. Idan kuwa hakan ya gagara, haka matsalar rashin aiki za ta ci gaba da girma shekara bayan shekara.”