Rashin amsa gayyatar ‘yan takara ba zai sa mu yi ƙasa a gwiwa ba – CITAD

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano

Dangane da cigaba da gayyato ‘yan takarkarun kujerar majalisar jiha da tarayya da jama’a ke yi don miqa qudurorin su ga ‘yan takarar da suka fito don wakiltar su.

Ita ma karamar hukumar Dala dake jihar Kano ta bi bayan ‘yan uwanta don gayyato ‘yan takarar daga kowa ce jam’iyya ɗan takara yake madamar ya fito da nufin ya wakilci wannan ƙaramar hukumar ta Dala.

A haka ne ma cikin irin ƙoƙarin al’ummar ne ranar Talatar nan suka gudanar da taron jin ra’ayoyin ‘yan takarar tare da miƙa nasu buƙatun don kawo cigaba, wanda aka gudanar da taron a ɗakin gabatar da musabaka dake ƙaramar hukumar ta Dala.

A jawabin Daraktan shirye-shirye na santar samar da cigaban harkokin fasaha da cigaban al’ummar da aka sani da CITAD, yayin taron Malam Isah Garba ya ce gaskiya ba su ji  daɗin yadda ‘yan takarar su kai burus da gayyatar yayin da ɗan takarar majalisar tarraya ne Hon Ali Rabiu Ali na Jam’iyyar PRP ya amsa wannan gayyata. 

Malam Isah ya ce wannan ba zai sare musu gwiwa ba za su isa zuwa gidajen ‘yan takarar da miqa buƙatun al’umma gare su tare da jin ta bakunan nasu. 

A nasa jawabin Maigirma wakilin Arewa na ƙaramar hukumar ta Dala Alhaji Sayyadi Muhammad Yola, ya ce taron wani matakin farko don haka taron yana da kyau amma abin takaicin da aka gayyaci ‘yan takara suka ƙi zuwa sai mutum ɗaya, amma kuma ya ƙara tabbatar da cewa za su sake kiran su don miƙa buƙatar da suke da ita.

Wakilin Arewan ya kuma bayyana cewa irin abinda ya faru a gurin taron na rashin halartar waɗanda aka gayyata “laifin su ne” dalili kuwa shi ne mutane ba su tsayawa su zaɓi wanda ya dace kawai sun zavar mutanen da ba su dace ba su tura su wakilce su.

Shi ma a nasa ɓangaren ɗan takarar da ya halarci taron daga jam’iyyar PRP Hon. Ali Rabiu Ali, da yake ma manema labarai ƙarin haske bayan kammala taron ya ce shi ana sa ra’ayi idan har zai kasa taimakon al’umma da suka tura shi wakilcin su ka da Allah ya ba shi nasara a wannan takara da yake yi.

Cikin irin ƙudurin da al’ummar ƙaramar hukumar Dala suka miƙa wa ‘yan takarar akwai batun tsaro, lafiya, ilimi, harkokin kasuwanci da bunƙasa harkokin noma da kiwo, sai batun ruwan sha da dai sauransu.