Rashin ciyarwa ne ke kai matan aure ga zina – Maryam Nadabo

“Kuskure ne kallon mutanen banza da ake wa mata ‘yan siyasa”

Daga AISHA ASAS

Ga dukkan alamu dai mata sun miƙe, sun kuma amince Allah na taimakon wanda ya tashi don neman na rufa wa kai asiri, duk da cewa, su na fuskantar ƙulubale a cikin wasu daga cikin ayyukan da suke zaɓa a matsayin sana’a, ba don komai ba kuwa sai don kasancewar su mata. A wannan satin, shafin Mata A Yau ya yi ma ku babban kamu da yake fatan ya zama barka da salla ga masu bibiyar jaridar Blueprint Manhaja. Fatan Allah ya maimaita. Ba kuwa kowa ba ce, face matashiyar da ta zama abin koyi ga matasan mata ‘yan’uwanta, kuma wadda ta zama baya da ta ke goya marayu har ma da masu uba. Maryam Yusuf Nadabo, matashiya ce da ta san muhimmancin neman na kai tare kuma da alfanun taimaka wa marasa hali. ‘Yar kasuwa ce, ‘Yar siyasa da ke fafutukar nema wa marasa galihu hanyoyin samun sauqin raɗaɗin talauci. A tattaunawar ta da Blueprint Manhaja, za ku ji irin yadda ta ke taimaka wa al’umma ta ɓangarori da dama tare kuma da shawarwarin da mu ke fatan su amfani mai karatu. Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Maryam Yusuf Nadabo:

MANHAJA: Mu fara da jin tarihin baƙuwar tamu.
MARYAM: Assalamu alaikum. sunana maryam Yusuf Nadabo. An haife ni a garin Kaduna. Na yi primary da secondary a Kaduna. Kuma na yi ‘School of Health’ a garin Kaduna. Na taɓa aure, tun Ina sakandare. Ina da yara uku. Namiji ɗaya, mata biyu. Ina tava kasuwanci da harkar siyasa da kuma harkar tallafi da na ke yi a ƙarƙashin gidauniyata mai suna Tallafi Foundation. A ɓangaren aure kuwa a yanzu ba na tare da mai gidana, uban ‘ya’yana kenan.

Me kika sa gaba a yanzu?
Gaskiya karatuna. Amma alhamdulillahi, a halin yanzu na yi jarrabawar ƙarshe. Sai kuma fatan mu ga alkhairi a nan gaba. Sai kuma harkokin da suka shafi gudanar da ayyukan gidauniya da mu ke yi, duk da cewa a baya gaskiya ababen sun fi tafiya a yadda mu ke so, kasancewar aiki ne na sa kai, domin mu da kanmu mu ke gudanar da ita, kuma da aljihunmu, ba wasu ne ke yi ba. To kasancewar yanayin rayuwa ya sauya, sai mu ka samu ɗan jinkiri, amma da yardar Allah, nan ba da jima wa ba za mu koma yadda aka saba ko ma fiye.

Duk da waɗannan abubuwan masu kyau ne, sai dai ba wanda ke tafiya ba tare da an kula da shi ba, don haka na riƙe kasuwanci gam! Domin ina harkar hijabai, kuma Ina da shagon ‘saloon’, inda mu ke gyaran kai da kuma kwalliya. Wani ɓangaren kuma Ina harkar rubutun littafan adabin Kano. Duk a ƙoƙarin ganin na dogara da kaina.

Wasu na ganin aikin tallafi ya fi raja’a ne kan tallafa wa mata kawai ba tare da kula buqatun maza ba. Shin menene gaskiyar zancen?
To, ya danganta da masu yi da kuma niyyar da suke da. Amma a na wa gani, dukka ɓangarorin biyu suna buƙatar tallafi. Idan mu ka yi duba da maza suke fita nema, ga kuma yanayin taɓarɓarewar tattalin arziki. Wani duk ƙoƙarinsa ba zai samu ba. To kinga a nan idan ba a taimaka masa ba, me iyalinshi za su ci. kinga kuwa taimakon magidanci ɗaya daidai yake da taimakon mace ɗaya zuwa uku da kuma yara, kinga kuwa yana da matuƙar muhimmanci.

Me ya ja ra’ayinki kika buɗe wannan gidauniyar?
Gaskiya ni Ina matuƙar son taimakon al’umma mussanma marasa ƙarfi. Ina da kishin al’ummata, Ina ƙaunar talakawa, Ina son in ga kowanne ɗan Adam ya samu madafa. kullum sai na yi wannan addu’a, Allah Ya ƙara hore min abinda zan taimaki jama’a. Wannan ne dalilina na son taimakon al’umma, kuma shine ya ja ra’ayina kan buɗe wannan gidauniyar.

A wani ɓangaren, ana ganin ki a wasu sha’ani na siyasa. Ko za mu iya jin irin rawar da kike taka wa a fagen siyasa?
Wannan gaskiya ne. Da farko dai ni mace ce mai son sha’ani na jami’a. Ina son mutane, kuma alhamdulillahi mutanen na sona. Mutum rahma ne, kuma tabbas Allah Ya ba ni wannan rahmar. Sanadiyyar jama’ar da na ke da na shiga harkar siyasa, don shige masu gaba tare da ganin sun samu abinda ya kamata a ce sun samu ba tare da cuta ko yaudara ba. Wannan dalilin ne ya sa in har mu ka ɗaga ɗan takara, to tabbas mutanenmu za su bi shi, za su karɓe shi hannu biyu, saboda sun yarda da mu.

Ko za mu iya jin irin nasarorin da kika samu a wannan tafiyar?
Alhamdulillahi ala kulli halin. Gaskiya zan iya cewa duk abinda na tunkara zanyi Allah Yana taimakona in yi. Wannan ce babbar nasarar da na ke kallo da ta fi kowacce.

Mutane da dama na yi wa matan da suka shiga sha’anin siyasa kallon marasa kamun kai, ko da kuwa suna ribatuwa da zaman matan a matsayin. Shin me za ki ce kan haka?
Gaskiya na ji daɗin wannan tambaya da kika yi Asas. Babban kuskure ne kallon mutanen banza da ake yi wa duk macen da ta shiga siyasa, domin ba a taru aka zama ɗaya ba. Kamar yadda aka sani, kowacce harka da ka sani ta duniya da mutane ke yi, za ka tarar akwai na ƙwarai akwai kuma mutanen banza, kinga kuwa bai kamata a ce ana yi wa matan da suke cikin harkar siyasa kuɗin goro ba, kamar yadda ake cewa, hali zanen dutse, duk inda ka shiga da halin na ka kake zuwa, don haka idan aka ce dukka to fa ba a yi wa saura adalci ba. Ta ɓangarena zan iya cewa, gaskiya alhamdulillah, domin duk inda na shiga a harkar siyasa, ana mutuntani tare da ba ni girma, hakan ba zai rasa nasaba da irin taka-tsantsan da na ke yi wurin ganin na kare martabata ta ‘ya mace, kuma wannan ba yi na ba ne, Allah ne Ya mani kariya. Kirana ga jama’a shine, su daina ɗaukarwa kansu kaya ta hanyar aibata kowacce mace da ke harkar siyasa.

A matsayinki ta mace, kin fuskanci ƙalubale a wannan fage?
Na samu gaskiya, kin san yadda aka ɗauki mata, musamman a arewacin ƙasar nan, da ta yi yunƙurin yin wani abu na inganta rayuwarta ko ta jami’a sai a fara surutai, kowa da irin abinda zai faɗa. Wasu su yi fatan alheri wasu savanin haka. Sai dai duk inda nasara ta ke dole akwai ƙalubale, don haka mun gode Allah.

A na ki gani, tsakanin cin zarafi na duka ko wulaƙantawa da kuma rashin abinci, wane ne ya fi kashe aure a Ƙasar Hausa?
Gaskiya rashin abinci, saboda da yawa mata wannan dalilin na rashin ciyarwa ya sa sun faɗa hallaka ta zinace-zinace, ba don suna da ra’ayin shashanci ba, sai don su samu abin kai wa ga bakin salati. Wasu ma ba don kansu suke yi ba, sai don sama wa ‘ya’yansu abincin. Duk da cewa wannan ba daidai ba ne, kuma ba hujja ba ce, sai dai abin takaicin, wasu magidantan da ke hana iyalansu abinci har da qeta ko lalaci, kana da shi, amma ka matse a jikinka kai kaɗai ke ci, ko ka zama mace, ba ka fita nema alhali ka ajiye mace da kuma ‘ya’ya. A taƙaice dai rashin abinci ya fi zama silar rabuwar aure, domin ɗan Adam zai iya jure duka da wulaƙanci, amma ba zai iya jure rashin abinci na wani lokaci ba.

Me mata suke sa ran samu daga mazajensu yayin da suka ɗauki tsayin lokaci suna zizara kwalliya?
Yabawa. Mace na son ta yi abu a yabe ta, a ɓangaren kwalliya tana so idan ta yi a ce ta yi kyau. “Ma sha Allah, baby kin yi kyau, kinga yadda kika haska kuwa, tamkar fa wata tauraruwa. Kai! Kin ko ji yadda kika rikita min zuciya. Baby I love you.” Ma’ana dai ya mata kalamai masu daɗi da za su sanya ta farin ciki, domin mace na son a koɗa ta, don haka za ka iya koɗa ta ko da bisa ƙarya ne, hakan zai sa ta ƙara dagewa wurin yi ma ka wadda ta fi, ba ma akan kwalliya ba kawai, idan miji zai dinga yaba wa matarsa a duk abin da ta yi masa, tabbas zai zama ɗan gata, domin a kullum za ta dinga ƙoƙarin ganin ta yi fiye da abin da ta yi. Sai dai kash! Ba kowanne namiji ne yake wannan ba, musamman ma mazanmu hausawa. Idan ka ji suna yaba wata to fa budurwarsu ce ko matan da ake haɗuwa a kafar sada zumunta.

Wane abinci kika fi so?
Shikafa da wake da mai da yaji da salat.

A ɓangaren tufafi wane ne zaɓinki?
Abaya.

Shin kina da ra’ayin tsaya wa takara a nan gaba?
Gaskiya a’a, ba ni da ra,ayi.

Ana ta fatawar mata sun yawaita, inda adadinsu ya zarta na maza. Shin a misali, za ki iya taimaka wa mijinki ya ƙara aure, tunda dai an ce ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne?
To fa! (dariya) Zan yi saboda Allah ne ya ce a yi. Ai gwara ta shigo ku zama ɗaya, da ya je yana leƙe-leƙe. Amma ni a yanzu ma na fi son in samu mai mata uku, in zama ta huɗu, kinga ta cikin sai ita ta taimaka in shigo, daga nan an rufe (dariya)

Mun gode.
Ni ma Ina godiya.