Rashin ilimin zaman aure ke jawo yawaitar mutuwar aure a ƙasar Hausa

Daga DAKTA ABDU ADAMU

A kwanakin baya na karanta wani rahoto ko sakamakon bincike da BBC Hausa ta wallafa wanda yake bayyana cewa, kusan kaso 32 cikin 100 na aure da ake yi a jihar Kano ba ya wuce wata uku zuwa wata shida ake raba auren. Wannan rahoto abu ne mai tsananin tayar da hankali.

Da farko dai, zan fara bayyana cewa, a ra’ayina shi saki a karan kansa ba aibu ba ne, musamman tunda Ubangiji ya halatta yin sa. Haka kuma dokar ƙasa ma ta bayar da dama a yi shi. Zan so mai karatu ya dan yi nazarin wannan misalin: Saboda wasu dalilai na al’ada da addini, za ka samu cewa da yawa masu shirin haɗa auratayya da juna a yankin nan namu na ƙasar Hausa ba sa samun damar fahimtar halayya da ɗabi’ar juna kafin su yi aure, idan ka kwatantasu da mutanen wasu yankunan. Yawanci ana gane halayyar juna ne bayan an yi aure. Sai dai daga baya za a iya gano wasu manyan matsaloli da ɗaya daga cikin ma’auratan wadanda ba za a iya warware su ba sai ta hanyar raba auren.

Ala ayyi halin dai, galibi sananun abubuwa ne suke haddasa saurin mutuwar aure, wanda wannan yana nuni ga cewa ma’aurata dama suna da ƙarancin fahimtar irin abubuwan da ake buƙata na jajircewa idan ana son zamantakewar aure ta yi ƙarko.

Da farko dai, mutane da yawa suna yin aure ba tare da sun fahimci irin tsananin hakuri da kau da kai da zaman aure yake buqata ba. Babu yadda za a yi ka zauna da mutumin da yanayin tasowarka da al’adun da ka saba da su suka bambanta, sannan  ka yi tsammanin cewa ba za ka ga wani abu a tattare da wannan mutumin wanda ya saɓa da yadda ka fahimci rayuwa ba. 

Misali, shekara kusan biyu mutum yake yi a makarantar raino/ nazare yana koyan ‘A B C’ tare da wasu tsirarun gajerun kalmomi. Idan kuwa haka ne, to shekara nawa kake tsammanin mutum zai ɗauka kafin ya gama karantar halayyar wani ɗan Adam ɗin da a da bai san shi ba?

Abin dai shi ne cewa dole ne sai ka damu da mutum, kana girmama shi, sannan kuma kana ƙaunar sa/ta kafin ka iya sanin yadda za ka iya haƙuri da kawar da kai da ake buƙata wurin iya zama da shi/ita. Shi aure kamar wani cikakken aiki ne mai zaman kansa da sai an mayar da hankali an yi shi tuƙuru, a inda kuma rayuwar soyayya ta saurayi da budurwa wani zama ne da ake yi na jin daɗi na wucin gadi. [Dole mu fahimci waɗannan bambance-bambancen].

Na biyu, maza da dama suna shigar da jiji da kai da faɗin rai a cikin mu’amalar rayuwar aurensu [su a dole sai sun nuna iko da sarauta]. Irin wannan kuma yana kawo wa aure gagarumin tasgaro. Kamata ya yi a ce daga ranar da mutum ya yi aure, to ya yi ƙowari ya dawwama a cikin auren. Ya bar matarsa ta zama ita ce mai gudanarwa da bayar da umarni a harkokin cikin gida. Kowanne (CEO) wato mai kamfani yana buƙatar manajan darakta! Ko ba haka ba?

Na uku, al’ummarmu ta fi mayar da hankali wurin nusar da mata a kan irin sadaukarwar da ake buƙata daga wurinsu a zaman aure. Amma sai dai ba a fiye mayar da hankali a wurin nusantar da maza a kan sadaukar da kan da su kuma ake buƙata daga wurinsu ba a zaman aure. 

A lokuta da dama akan manta da muhimmancin farin cikin mace a rayuwar aure. Wannan yake sawa maza da dama suke shiga rayuwar aure a makance kawai suna tsammanin cewa idan suka yi aure za a kawo musu wata mace ce wacce sai yadda suka yi da ita kamar wata mutum-mutumi (robot). Maza da dama sukan jawo ayoyin Al-Ƙurani da suke nuna fifikon namijin a zaman aure ba kuma tare da sun fahimci irin siyasar da ake buƙata wurin riƙe aure ba. 

Babban abinda ya kamata ka fahimta a matsayinka na namiji sadaukar da kan da za ka yi [ka yi haƙuri da jin daɗinka, da son zuciyarka don aurenka ya yi ƙarko], hakan shi ne zai taimaka wurin saka aurenka ya yi ƙarko. Kasancewar cewa igiyar aure a hannunka take, shi zai nuna maka cewa riƙe auren da ƙarkonsa shi ma aikinka ne.

Abu na gaba, sau da dama al’ummarmu suna nuna cewa aure kamar wani alfarma ce ake yi wa mace idan aka yi shi. Duk da cewa a wasu lokutan auren ya kan iya kasancewa alfarma, musamman idan aka kalli bambancin tattalin arziki da yake tsakanin maza da mata a wasu lokutan, ba ko da yaushe ne aure yake kasancewa alfarma ga mace ba. 

Maza da dama sukan yi amfani da wannan bauɗaɗɗen tunanin na cewa duk macen da suka aura, alfarma suka yi mata su mayar da kansu kamar wasu alloli a gidajen aurensu. 

Sai dai mata da dama sun fara nuna rashin yardarsu da irin wannan tunanin na ƙasƙantar da mace a gidan aure, musamman saboda ƙarin ilimi da wayewa. Abin dai shi ne, yana da kyau mutane su fahimci cewa, ana yin aure ne saboda a samu nutsuwa da kwanciyar hankali sannan kuma don a samu ‘ya’ya magada.

Aure ba wata hanya ba ce da ake bi wurin zama alloli. Gidanka kuma bai kamata ka mayar da shi kamar wani wurin bauta ba. Sannan bai kuma kamata ka riƙa cin burin za a bauta maka a cikin gidanka kamar wani gunkin bauta ba (saboda ana jin tsoronka).

Abin takaicin shi ne, babu wata hanya mai sauƙi ta magance wannan matsalar. Dole ne sai mutane sun koma zuwa ga tushe don gyara matsalolin nan. Fata na shi ne, wannan bincike da aka yi a kan yawan mutuwar aure ya buɗe mana idanu, mu yi wa fahimtarmu a kan zamantakewar aure garambawul.

Kula: wannan ra’ayina ne kawai na ƙashin Kai na faɗa ba wai don ni ƙwararre ne a kan harkar auratayya ba. Allah ne masani.

Dakta Abdu Adamu shi ne ya rubuta cikin harshen Ingilishi shi kuma abokinsa Dakta Abdulazeez Tijjani ya fassaro. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *