Rashin son karatu da taɓarɓarewar ilimi

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Mai karatu na san a yayin da ka ke karanta wannan rubutu nawa na yau, idan kai magidanci ne mai iyali yaran ka yanzu sun koma makaranta ko suna shirin komawa, bayan dogon hutun da aka yi. Na san yanzu ba za ka kasa lissafin irin kuɗaɗen da ka kashe wajen shirin komawarsu makaranta, kama daga kuɗin makaranta na shiga sabon aji, ko sabbin shiga, da tsarabe-tsaraben da duk uba ko uwa ke fargabar lokacin zuwan su ba. Saboda yadda iyaye ke kai gwauro da mari suna haxa ƙanana da manya don su iya biyan kuɗin makarantar ‘ya’yansu, domin su sauke nauyin da ke kansu na samar musu da ilimi mai inganci, da ake sa ran zai kyautata rayuwarsu ta gobe.

Wannan lokaci ne mai matuƙar daga hankali ga iyaye, musamman masu ƙaramin ƙarfi, da ke da burin ganin ba a bar yaransu a baya ba, a kokawar samar wa ‘ya’yansu ingantacciyar rayuwa, kasancewar ilimi ya zama ƙashin bayan cigaban kowanne ɗan Adam da kowacce al’umma. Kuma kamar yadda ya ke a ƙudiri na hudu na sharuɗɗan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta gindaya wa ƙasashe su tabbatar kowanne yaro ya shiga makaranta kuma ya samu ilimi mai inganci. Ko da yake haƙƙi ne na gwamnatocin ƙasashe su samar da tsari da muhallin da kowanne yaro ko yarinya zai samu ilimi nagartacce, da zai mori rayuwarsa ta duniya da shi.

Sai dai a yayin da gwamnatoci a Nijeriya suka gaza wajen sauke nauyin da ke kansu na samar wa yara a kowanne lungu da ƙauye na ƙasar nan ’yancin da haƙƙin shiga makaranta, don yin karatu. Saboda ƙalubalen rashin makarantu masu inganci, rashin kyakkyawan albashi ga malamai, rashin samun damar tura malamai kwasa kwasai na ƙaro ilimi, da gogewa kan sabbin dabarun koyarwa na zamani, ga kuma rashin kayan koyarwa, kujerun zama da sauran muhimman buƙatun na malanta.

Talakawa sun gaji da jiran gawon shanu, don ganin gwamnati ta ba da ƙarfi da muhimmanci ga harkar ilimi, kamar yadda a kowanne lokaci take nanatawa. Ba zai yiwu a ce gwamnati ba ta komai a harkar ilimi ba, musamman ta ƙarƙashin Hukumar Kula da Ilimin Vai Ɗaya da ke jihohi (SUBEB) wanda ke kula da ƙananan makarantu na firamare da ƙaramar sakandire. Sai dai ƙoƙarin da ake yi har yanzu bai isa ba, kuma kason da ake warewa ilimi a kasafin kuɗin kasa duk shekara, ba ya zuwa ko ina. Yawaitar tafiya yajin aiki da ƙungiyoyin malamai a matakai daban-daban ke yi ya sa tsarin ilimin kullum sai baya ya ke daxa yi.

Iyaye sun gaji da ganin koma bayan yanayin karatun ‘ya’yansu, sun gwammaci mayar da ‘ya’yansu makarantun kuɗi na masu zaman kansu, ko da kuwa gogewarsu ba ta kai yadda ake buƙata ba, duk kuwa da irin tsadar da makarantun ke da su. Dole ne a jinjinawa iyayen yara masu ƙaramin ƙarfi bisa la’akari da yadda suke sadaukarwa kan karatu, tarbiyya da kula da sauran buƙatun iyali, duk kuwa da irin yadda rayuwa ke ƙara tsada a ƙasar nan. Abubuwan da mutum ke ganin damarsu a baya, yanzu sun fi ƙarfinsa.

Lamarin ya kai ga wasu iyayen suna raba ɗawainiyar kula da karatun yara, idan uba ya ɗauki nauyin wasu to, tilas uwa ma ta ware wasu yaran da za ta ɗauki nauyinsu. Ko kuma ta ɗauki wani vangare na kula da hidimar gida. Wannan ga iyali masu dama-dama kenan, ko waɗanda uwa da uban ke aiki. Amma ga waɗanda hannu bai cuɗi baya ba, saboda tsananin rayuwa sai dai a ware wasu yaran da ake ganin sun fi fahimta a sa su a makarantar kuɗi, wasu kuma a barsu a ta gwamnati, ko kuma wasu a kora su wajen koyon sana’a, wasu na boko wasu kuma talla. Subhanallah!

Wasu gwamnonin Nijeriya sun sanya dokar ba da ilimi kyauta kuma dole ga kowanne yaro da ke jiharsu, daga matakin firamare zuwa ƙaramar sakandire, amma sun kasa kula da tsarin gudanar da makarantun, duba da irin lalacewar da gine ginen makarantun suka yi, rashin kujerun zama, rashin littattafan karatu, rashin kyakkyawan makewayi da rashin tsafta, rashin muhallin da ya dace a koyar da yara su amfana da karatun da ake koyar da su. Duk kuwa da kasancewar gwamnatin tarayya ta ce tana kashe abin da ya kai Naira biliyan ɗaya a kowacce rana, don ciyar da ɗaliban wasu makarantun firamare da aka ware ana ciyar da su abincin rana, wanda suka kai har Miliyan 10, kan kuɗi Naira ɗari ga kowanne yaro.

Amma duk da haka akwai yara da shekarun su bai wuce 5 zuwa 14 ba, da suka zarta yawan adadin waɗanda aka ce ana ciyar da su abincin rana, don su daure su zauna a makaranta su yi karatu. Sakamakon binciken ya nuna cewa yara Miliyan 10 da dubu 500 ne suke rayuwa ba tare da sun zauna a makaranta sun koyi wani ilimi ba, sai yawo a titi. Yayin da su ma waɗanda ke karatun sukan kashe shekaru fiye da adadin da ya kamata suna makaranta, ba tare da sun gama ba, saboda yaje yajen aiki, rikice-rikicen addini, siyasa da tarzomar ‘yan makaranta.

Duk ƙoƙarin da ake cewa gwamnati na yi, da dagewar da iyaye ke yi, har yanzu Nijeriya na sahun baya wajen bai wa harkar ilimi muhimmanci. Ƙaramin Ministan Ilimi
Goodluck Opiah ya koka da yadda ake ci gaba da samun koma baya a harkar ilimi. Ya bayyana ƙiyasin da aka yi na cewa, a wannan shekara kaɗai, kimanin kashi 38 cikin ɗari na ‘yan Nijeriya ba su iya karatu da rubutu ba, adadin da aka ce ya kai mutane Miliyan 76. Yayin da kaso mafi girma daga cikin wannan adadi ƙananan yara ne, da suka kai Miliyan 6 da dubu ɗari 7. Ya danganta ƙaruwar hakan kan talauci, da yawan iyaye marasa ilimin boko, da ba su koyi karatu da rubutu ba.

Rahoton da wata ƙungiyar Majalisar Ɗinkin Duniya mai bincike kan cigaban harkokin ilimi a duniya, ya gano cewa Nijeriya ita ce ƙasa ta 161 daga cikin ƙasashen duniya 189 da suke fuskantar taɓarɓarewar ilimi, abin da ke nuna tsananin lalacewar da ilimi ya yi da ƙalubalen da hakan ke nunawa, ga cigaban makomar ƙasar nan.

Abin da ke nuna cewa, lallai akwai matsala mai yawa da ke tunkarar ƙasar nan, a dalilin ƙaruwar da za a samu ta yara masu yawo a titi babu karatu, da masu barin makaranta, ba su kammala ba, duk saboda rashin kuɗin biyan kuɗin makaranta da ɗawainiyar karatu. Yara mata sun zama karuwan ƙarfi da yaji a cikin makarantu da cibiyoyin ilimi, saboda gazawar iyayensu wajen iya ɗaukar nauyin karatunsu, don haka in dai sun gwammaci su yi karatun to, kuwa za su bi maza ko bai wa malamai haɗin kai, domin su samu abin da suke so. Yayin da ɗalibai maza da suke makaranta wasu ke sace-sace da fashi da makami, ko yanzu da harkar satar mutane don neman kuɗin fansa ta yi yawa. Wasu matasan kuwa yanzu sun koma noma ko kasuwanci, wasu kuwa musamman mata sun yi aure an fara zuba ’ya’ya.

Babban misali ma dai shi ne dogon lokacin da aka kwashe ana yajin aikin ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU, wanda ya zaunar da miliyoyin ɗalibai a gida, waɗanda akasarin su ‘ya’yan talakawa ne, suna watangaririya a titi, saboda zaman gida da rashin makaranta. Wasu ma har sun fara fitar da rai daga karatun jami’a gaba ɗaya, wasu da iyayen su ke da hali sun mayar da su jami’o’i masu zaman kansu. Wasu an musu aure, sun gwammace gidan miji da jiran boko, masu ɗan zurfin tunani ne ma suke buɗe wuraren sana’o’in hannu ta amfani da basirar su da kuma ayyukan da suka koya don hana zaman banza da samun abin dogaro.

A nan ba ina son in goyi bayan ƙungiyar ASUU ko Gwamnatin Tarayya, kan wanda ke da laifi ko wanda ya yi daidai a wannan taƙaddama ba ne. A rubutuna na baya na yi tsokaci a kan haka, amma abin da na ke so in nuna a nan shi ne kowanne ɓangare akwai abin da ya dogara shi, kuma yana ganin shi ne kawai mafita ga cigaban harkokin ilimi a ƙasar nan. Sai dai a yayin da suke wannan taƙaddama da ta shafe tsawon watanni ana yi, abin dubawa a nan shi ne illar da hakan ke haifar wa a kan ɗalibai da iyayensu ba ƙarama ba ce. Malamai za su iya cewa cikin lokaci kaɗan za su yi wa ɗalibai bitar karatun baya da wanda aka wuce ba a yi ba, ba tare da matsala ba, amma wata illar da ta afku a dalilin wannan yajin aiki, da cire karsashin karatu a zukatan matasa, da zubewar kimar karatun jami’a a wajen wasu ɗalibai da iyaye, ba zai taɓa dawowa ba.

A wani ɓangare na ƙoƙarin da Majalisar
Ɗinkin Duniya ta ke yi na ganin yara ‘yan mata da ake cirewa daga makarantu da niyyar a yi musu aure, ko don ana ganin karatun mace ba wani tasiri ne da shi ba, ko don saboda talauci, sun samu tallafi wajen ɗaukar nauyin karatunsu, da mayar da su makaranta don su ci gaba da karatu har su ƙarasa babbar sakandire, mai laƙabi da AGILE a takaice shi ma yana fuskantar tasgaro, domin kuwa a halin yanzu son zuciya, kwaɗayi, da rashin kishin ƙasa yana durƙusar da shirin, wanda aka fara shi a wasu jihohin Nijeriya cikin kwakkyawar niyya, shi ma da ayar kwalliya ta biya kuɗin sabulu. A hankali miliyoyin dalolin da aka zuba cikin shirin, cin hanci da rashawa na so ya nakasa shi.

A yayin da dakarun tsaron Nijeriya ke cin galaba a yaƙin da suke yi da ‘yan ta’addan Boko Haram, waɗanda suke ƙoƙarin kawo wata bahaguwar aƙida ta hana karatun boko, da zimmar cewa, yana rusa tarbiyya da koyarwar addinin Musulunci. Lallai ne kuma Gwamnatin Tarayya ta karkato da hankalinta, wajen zuba jari da inganta harkar ilimi, bunƙasa ilimin kimiyya da fasaha, don farfaɗo da ƙere-ƙere da raya ƙasa. A dawo da darajar da aka san makarantun gwamnati da shi, daga firamare, sakandire har jami’a da manyan makarantun ilimi. A dawo da ayyukan hukumar kula da yaqi da jahilci, don manyan da shekarun su suka data, kuma ba su koyi karatu da rubutu ba, su samu damar samun ilimi mai inganci da za su yi amfani da shi, wajen ba da gudunmawa ga cigaban ƙasa.

Muna fatan Allah ya ƙarfafa gwiwar gwamnatin Nijeriya ta tashi tsaye ta yi abin da ya dace, na ceto rayuwar ‘yan Nijeriya daga talauci, jahilci, da rashin tabbas ɗin da ƙasar nan ke ciki. Su kuma iyayen da suke cigaba da faɗi tashin yadda za su kula da karatun ‘ya’yansu, don su samu ilimi mai inganci da kyakkyawar rayuwa, Allah ya buɗa musu, ya hore musu abin da za su ci gaba da ƙoƙarin sauke nauyin da ke kansu. Ya sa wa iyalinsu albarka. Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *