Rasuwar Momoh: Na rasa babban amini – inji Buhari

Daga UMAR M. GOMBE

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa dangane da rasuwar amininsa Prince Tony Momoh.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya fitar a Litinin da ta gabata a Abuja, Shugaba Buhari ya bayyana cewa, marigayin ya kasance tare da shi a duk faɗi-tashin da ya sha.

Yana mai cewa, “Samun kwatankwacin marigayin wajen biyayya a fagen siyasa, abu ne mai wahalar gaske. Zan yi rashin sa matuƙa.”

Jaridar Manhaja ta kalato Buhari ya yi tuna baya inda ya ce, “Marigayi Momoh ya ba da gagarumar gudunmawa a matsayinsa na Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulda da Jama’a na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen jam’iyyar ANPP a zaɓuɓɓukan 2003 da 2007.”

A halin rayuwarsa, marigayin ya taɓa rike mukamin Ministan Labarai da Al’adu, haka ma muƙamin ciyaman na jam’iyyar CPC da dai sauransu.

A cewar Shugaba Buhari, da gudunmawar Momoh wajen kafa jam’iyyarsu ta APC.

Daga nan, Buhari ya jajanta wa masana’antar yaɗa labarai bisa rasuwar Momoh wanda tsohon ɗan jarida ne da ya taka rawar gani wajen cigaban aiki jarida Nijeriya.

Kazalika, shugaban ya miƙa ta’aziyyarsa ga Masarautar Auchi da gwamnatin jihar Edo da ma al’ummar jihar bakiɗaya dangane da rasuwar aminin nasa.