Rasuwar Sani Buhari Daura babban rashi ne ga Nijeriya – Shugaba Buhari

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana rasuwar hamshaƙin ɗan kasuwar nan mazaunin Kano, Alhaji Sani Buhari Daura, a matsayin babban rashi ba ga jihar Katsina da Kano kaɗai ba, amma ga ƙasa bakiɗaya musamman ma idan aka yi la’akari da irin tasirin da yake da shi ga tattalin arzikin ƙasa.

Buhari ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta sami sa hannun mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu a ranar Lahadi. Yana mai bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin daɗaɗɗun jiga-jigan ‘yan kasuwa a Nijeriya waɗanda suka bada gudunmawarsu gaya wajen cigaban tattalin arzikim ƙasa tare da samar da ɗauruwan guraben aiki ga jama’a.

Ya ce mutane irin su Marigayi Sani Buhari sun ɗaukaka ne saboda ƙwazonsu da kuma sadaukarwa.

Kazalika, Buhari ya ce rayuwar marigayin cike take da nasarori saboda yadda ya kasance mutum mai ƙoƙari a halin rayuwarsa.

Daga bisani, Shugaba Buhari ya yi amfani da wannan dama wajen isar da ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da ke Daura da Kano, haɗa da gwamnatoci da ma al’ummar garuruwan biyu dangane da wannan babban rashi.

A safiyar wannan Lahadin Allah Ya yi wa Alhaji Sani Buhari Daura cikawa a ƙasar Dubai, inda ya bar duniya yana da shekara 90.