Rayuwa na ƙara tsananta yayin da aka shiga kwanaki da yawa babu lantarki a Arewa

Daga USMAN KAROFI

Yankin Arewa na Nijeriya ya shiga rana ta takwas ba tare da wutar lantarki ba, wanda hakan ya haifar da cikas mai tsanani ga ayyukan yau da kullum da rayuwar jama’a. Rashin wutar ya samo asali ne daga matsalar wutar 330kV da ke tsakanin Benue da Enugu, da kuma layin Shiroro da Kaduna, wanda ya jefa yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, da kuma wani sashi na Arewa maso Tsakiya cikin duhu.

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Nijeriya (TCN) ya bayyana cewa layin wutar 330kV DC Ugwaji-Apir ya samu matsala, wanda ya jefa yankin Arewa gaba ɗaya cikin duhu. Wannan matsalar ta shafi asibitoci da ɗakunan gwaje-gwaje waɗanda ke buƙatar wutar lantarki mai ƙarfi don na’urorin aikin kiwon lafiya da gwaje-gwaje, inda hakan ke kawo jinkiri a aikin kula da marasa lafiya.

Kasuwanni na cikin yanayi na fargaba, musamman masu sayar da abincin sanyi irin su kifi da kayan ganye, waɗanda suka ce sun yi asarar kaya saboda rashin wutar da za su iya ajiye su cikin firinji. Haka kuma, masu samar da ruwa sun yi nuni da cewa farashin ruwan da suke siyarwa ya ninka saboda ƙarin kuɗin da suke kashewa wajen amfani da janareto wajen aikin rijiyoyi.

Ɓarayi kuma sun samu dama inda suka ci gaba da lalata layukan wuta da sauran kayan aikin wuta. Wannan ya kara jefa yankin cikin wahala wajen dawo da wutar, duk da kokarin da TCN ke yi. A cewarsu, lamarin ya ɗauki lokaci saboda matsalar rashin tsaro da kuma lalacewar kayan aiki.

Wasu asibitoci kamar Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) sun fuskanci matsalar kuɗin siyan man dizal na sama da N500,000 a kullum don tafiyar da janareto, yayin da ake amfani da na’urorin hasken rana don gaggawa. Marasa lafiya sun koka game da yawaitar sauro a ɗakin kwana wanda ke ci gaba da matsawa idan aka kashe janareto da daddare.

A jihar Gombe, masu siyar da kifin sanyi sun bayyana asarar da suke samu yayin da suke amfani da janareto don adana kifin. Wani mai siyar da kifi ya ce ya na kashe kuɗin mai sosai don ci gaba da adana kayansa, wanda hakan ke ƙara farashin kayan sa, lamarin da ke rage yawan kwastomomi.

Haka kuma, masana’antu da sana’o’in gargajiya da ke dogaro da wuta irin su masaka, itace da sauran ayyuka a Jos sun yi asarar kwastomomi. Yan daba sun kuma lalata wasu na’urorin wuta a unguwanni kamar Anguwan Rogo da Gangare, wanda ya jefa al’ummomi cikin duhu.

Ƙungiyar Sanatocin Arewa sun nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta dawo da wutar a yankin Arewa, musamman ta hanyar gyaran layin wutar Shiroro-Kaduna.