Rayuwar ƙarya ’yan Nijeriya ke yi kafin cire tallafin fetur – Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa, ’yan Nijeriya da dama na rayuwar “ƙarya” ne kafin a cire tallafin man fetur, matakin da ya ce ya zama dole domin hana ƙasar faɗawa cikin matsalar tattalin arziki.

Da yake jawabi yayin wani taron na jami’ar Fasaha ta Tarayya ta Akure (FUTA) da ke Jihar Ondo, Shugaban ƙasar ya bayyana cewa matakin da gwamnatinsa ta ɗauka na cire tallafin man fetur da kuma haɗa farashin canji ya biyo bayan buƙatar gaggawa na ceto makomar Nijeriya.

Tinubu wanda mataimakin shugaban jami’ar Ilorin ya wakilta, Farfesa Wahab Egbewole, SAN, ya bayyana cewa tallafin, duk da cewa an yi nufin tallafa wa talakawa ne, yana ƙarewa ne ga masu hannu da shuni, wanda ya bar talakawan Nijeriya cikin halin la’haula.

“Kamar yadda kuka sani, mun karɓi ragamar mulki ne a daidai lokacin da tattalin arzikinmu ke neman durƙushewa sakamakon ɗimbin basussuka na tallafin mai da dala,” inji shi.

“An ba da tallafin ne don tallafa wa talakawa da kuma kyautata rayuwa ga dukkan ‘yan Nijeriya. Abin takaici, su na rayuwar ƙarya wanda hakan zai iya kai ƙasar nan ga rugujewa gaba ɗaya, sai dai idan an ɗauki tsauraran matakai cikin gaggawa ba,” inji shi.

Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa tuni manufofin da gwamnatinsa ta aiwatar suka fara haifar da sakamako, da alamun farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

Ya bayyana cewa, ma’aunin tattalin arzikin ƙasar yana inganta, yayin da tsarin tattalin arziki ke canjawa zuwa wani yanayi mai ban sha’awa.